Akalla sama da mayaƙa 400 da suke addabar yankunan arewacin jamhuriyar Nijar suka miƙa wuya a birnin Agadez, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ƙasar, ANP ta ruwaito.
Rahoton ya ƙara da cewa mayaƙan ƴan ƙungiyar Patriotic Liberation Front da Movement for Justice and Rehabilitation of Niger ne.
An ce mayaƙan sun amince da kiran da shugaban ƙasa Janar Abdourahmane Tchiani yayi musu na su ajiye makamai su miƙa wuya.
Ba a taɓa samun mayaƙa da suka kai wannan adadin ba, sannan a ranar 3 da 11 ga watan Nuwamba ma an samu irin hakan, inda wasu mayaƙan daban suka miƙa wuya a birnin na Agadez.
Mayaƙan suna faɗa ne tare da kira da a saki shugaban ƙasa Mohamed Bazoum da aka hamɓarar.