Wednesday, April 15, 2026
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiGwamna Buni Zai Gwangwaje Matasan Yobe  Da Keke Napep 100, Baburan Jega...

Gwamna Buni Zai Gwangwaje Matasan Yobe  Da Keke Napep 100, Baburan Jega 80

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu

A ci gaba da kokarinsa na ganin an samar da karin ayyukan yi ga matasa, gwamnan jihar Yobe,  Mai Mala Buni, ya amince da sayo baburan KEKE NAPEP 100 da baburan JEGA samfurin akori kura masu tayoyin uku guda 80 domin karfafa gwiwar matasa don samun abin yi a jihar.

Kwamishinan ma’aikatar samar da arziki  da aikin yi na jihar Yobe, Aji Yerima Bularafa ne ya bayyana haka, a lokacin da yake zantawa da manema labarai irin nasarorin da wannan gwamnati ta samu a fannin inganta rayuwar al’umma.

A cewar kwamishinan, kafa ma’aikatar samar da arziki da aikin yi na daga cikin kokarin da gwamnatin jihar ke yi na farfado da tattalin arzikin al’umma, musamman wadanda rikicin, ‘yan tada kayar baya ya shafa wanda ya kai ga lalata harkokin ‘yan kasuwa, ta hanyar shirye-shiryen karfafa gwiwar ‘yan kasuwa.

Kwamishinan ya kara bayyana cewa, a kwanakin baya ne gwamnatin jihar ta bayar da wasu kwangiloli hudu dabam-dabam ta hannun ma’aikatar don sayo kayayyakin karfafa gwiwarl da tallafawa kananan ‘yan kasuwa da wasu masu hannu da shuni da sauran su da suka kai sama da Naira biliyan 8.

Don haka ya bukaci jama’a da su yi hakuri, yana mai cewa shirin wani tsari ne na ci gaba da kan zo bi da bi.

Kwamishinan ya kara da cewa babu wani dan Yobe  da za a hana shi samun tallafin da gwamnatin jihar ta bayar in Allen ya so.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments