Tuesday, September 1, 2026
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeSiyasa"Zan Riƙa Turawa Ƙananan Hukumomi Kuɗaɗensu Kai Tsaye Idan Na Zama Shugaban...

“Zan Riƙa Turawa Ƙananan Hukumomi Kuɗaɗensu Kai Tsaye Idan Na Zama Shugaban Ƙasa 2027”, In Ji Atiku

‎”Zan Riƙa Turawa Ƙananan Hukumomi Kuɗaɗensu Kai Tsaye Idan Na Zama Shugaban Ƙasa 2027″, In Ji Atiku

Daga Aliyu Bala Gerengi a Gombe

‎Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin cewa zai tabbatar da tura kuɗaɗen da ake ware wa ƙananan hukumomi kai tsaye zuwa asusunsu, idan ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

‎Atiku ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da kakakinsa, Kenneth Okonkwo, ya wallafa a shafin X ranar Talata,

‎Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce gwamnatinsa za ta mutunta hukuncin kotu tare da tabbatar da cikakken ƴancin cin gashin kai na ƙananan hukumomi.

‎Ya kuma zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da gazawa wajen aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli na Yulin 2024 da ya tabbatar da ƴancin cin gashin kan kuɗaɗen ƙananan hukumomi.

‎Atiku ya ce bai wa ƙananan hukumomi kuɗaɗensu kai tsaye zai taimaka wajen kawo ci gaba a ƙauyuka da garuruwa, rage talauci da kuma ƙarfafa ƙananan hukumomi wajen yaƙi da miyagun laifuka da ta’addanci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments