Daga Aliyu Bala Gerengi a Gombe
Majalisar Ƙoli ta Shari’a a Najeriya (SCSN) ta yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da cikakken bin doka da oda a kan ci gaba da tsare tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufa’i.
Majalisar ta bayyana damuwa kan halin da ake ciki game da ci gaba da tsare El-Rufa’i, musamman abin da ta bayyana a matsayin wahalar cika sharuɗɗan beli da aka gindaya masa.
A cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Majalisar, Nafiu Baba Ahmad, mni, ya fitar a ranar Litinin, Majalisar ta ce kamar kowane ɗan Najeriya, El-Rufa’i yana da haƙƙin da Kundin Tsarin Mulkin ƙasa ya ba shi, kuma ana ɗaukar mutum ba shi da laifi har sai kotun da ke da hurumin shari’a ta tabbatar da hakan.
Majalisar ta jaddada cewa Najeriya ƙasa ce da ke tafiyar da tsarin dimokuraɗiyya bisa kundin tsarin mulki, inda dole ne a mutunta ka’idojin bin doka, sauraron shari’a cikin adalci da kuma tsare mutum bisa ƙa’ida, ba tare da la’akari da matsayinsa, jam’iyyarsa ko ra’ayinsa na siyasa ba.
Ta ce ba ta goyon bayan aikata laifi ko nuna ƙiyayya ga doka ta kowace hanya, amma ta ƙara da cewa neman tabbatar da adalci shi ma ya kamata ya kasance cikin adalci da bin doka.
Majalisar ta yi gargaɗin cewa duk wani mataki da ake ganin an ɗauka ba bisa ƙa’ida ba ko kuma saboda dalilan siyasa, na iya rage amincewar jama’a ga hukumomin gwamnati tare da raunana tsarin dimokuraɗiyya.
Saboda haka, SCSN ta buƙaci hukumomin da abin ya shafa su gudanar da al’amuransu cikin tanadin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya da sauran dokokin ƙasar, tare da tabbatar da cewa an bi matakan doka a kowane mataki.
Haka kuma, Majalisar ta yi kira ga hukumomi da su guji duk wani mataki da ka iya sa a zarge su da tsangwamar El-Rufa’i saboda dalilan siyasa, tana mai buƙatar a tabbatar da adalci, gaskiya da kuma bin doka.
Majalisar ta ce haɗin kan Najeriya da zaman lafiyar ƙasar na dogaro matuka da sahihancin hukumominta da kuma irin amincewar da jama’a suke da ita a kansu.
Ta jaddada cewa ba wai kawai ya kamata a yi adalci ba, har ma ya zama a bayyane ga jama’a cewa an yi adalcin, tana mai cewa yin amfani da doka cikin adalci, ba tare da nuna bambanci ba, shi ne ginshiƙin haɗin kan ƙasa da ci gaba mai ɗorewa.
Majalisar ta sake jaddada aniyarta ta kare adalci da haƙƙin ’yan ƙasa, tare da inganta zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al’ummar Najeriya.
Ta kuma yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su kasance masu natsuwa da ɗaukar alhaki, tare da tabbatar da cewa dukkan matakai da za su ɗauka sun dace da tanadin doka.


