Saturday, June 13, 2026
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiFARASHIN DABBOBI YA SAUKA A KASUWAR MAI’ADUA A JIHAR KATSINA

FARASHIN DABBOBI YA SAUKA A KASUWAR MAI’ADUA A JIHAR KATSINA

Daga: Bashar Isah Daura

Yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen bukukuwan Sallah da kuma ibadar layya ga Musulmi, an samu saukin farashin dabbobi a kasuwar dabbobi ta Mai’adua da ke jihar Katsina, a ranar Lahadi 24 ga watan Mayu, 2026. Masu saye da sayarwa sun bayyana cewa farashin shanu da sauran dabbobin layya ya dan sauka idan aka kwatanta da makonnin baya.

Malam Abubakar Muhammad, Sarkin Shanun Mai’adua, ya shaida wa wakilinmu Bashar Isah Daura cewa karuwar shigo da dabbobi cikin kasuwar na daga cikin abubuwan da suka taimaka wajen samun saukin farashin, duk da yadda ake ci gaba da samun masu saye daga sassa daban-daban.

Ya kara da cewa rashin isassun kudi a hannun jama’a yana daga cikin dalilan saukar farashin dabbobin, sannan hadakar mutane biyu ko fiye wajen sayen dabbar layya guda shi ma ya taimaka wajen raguwar farashin.

Haka nan, tsadar abincin dabbobi a halin yanzu ta taimaka wajen rage farashin dabbobin a bana.

Shi ma Abubakar Na Munau, daya daga cikin masu fada a ji a bangaren kasuwancin dabbobi, ya bayyana cewa ragon da a baya ake sayarwa kan naira dubu dari da hamsin, yanzu ana samun sa kan naira dubu dari da goma. Haka nan timkiya ma ta samu saukin farashi. Ya kara da cewa akuyar da a baya ake tsammanin za ta kai naira dubu dari daya, yanzu ana iya samun ta kan naira dubu saba’in.

Sai dai wasu masana kasuwar dabbobin sun ce ana sa ran farashin zai iya canzawa a ranakun yanka.

Wani daga cikin dillalan dabbobi a kasuwar, Malam Sadiku, ya bayyana cewa saniyar da ake sayarwa kan naira dubu dari bakwai yanzu ta dawo naira dubu dari biyar da hamsin. Haka kuma saniyar da ta kai naira miliyan daya da dubu dari biyar ta dawo naira miliyan daya da dubu dari uku, haka ma rakumma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments