Daga; MUHAMMAD KAWU, Bauchi
Babbar Kotun Tarayya dake zama a birnin Tarayya na Abuja a jiya Alhamis ne ta nusar da cewar, Sanata David Mark shine sahihin shugaban Tarayya na Jam’iyyar ADC (African Democratic Congress).
Rahotanni sun riwaito da cewar, Mai Shara’a Musa Liman ya kuma kori qarar da Wakili Leke Abejide ya gabatar wa kotu yana qalubalantar kasancewar David Mark da Ogbeni Rauf Aregbesola a matsayin shugaba da sakayare jam’iyyar na qasa.
Mai Shara’a Liman sai ya xabbaka rashin yarda ko turjiya da jam’iyyar ADC, Ralph Nwosu, Mark and Aregbesola suka tokarar, suna mai cewar, qarar bata da tushe, balle makama.
Alkalin ya kuma yi hukunci da cewar, Kotun sa bata da hurumin yin katsalandan wa lamuran cikin gida na Jam’iyyar.Ya kuma yi nuni da cewar, Abejide ya gaza nuna inda ko alamar dake nuna cewar, shugabancin Mark wa jam’iyyar yayi wa ‘yanchin sa katsalandan.
Ya kuma yi la’akari da cewar, miqa shugabancin jam’iyyar da Nwosu yayi wa Mark bai yi karantsaye was kundin tsarin milkin jam’iyyar ta ADC ba.
Alkali Liman ya kuma bayyana cewar, taron masu ruwan da tsaki da aka gudanar a ranar 2nd ga Watan Yuli na shekarar 2025 shine gaba ga, ko ya riga taron majalisar qoli na jam’iyyar ta ADC wanda aka gudanar a ranar 29 ga Watan Yuli, 2025 wanda ya gabatar da Mark da Aregbesola.
Kotu ta ayyana cewar kasancewar Mark da Aregbesola a matsayin shugabanni yana bisa ka’ida, kuma ya tafi sarmadan da tanadin kundin tsarin milkin qasa, dokar zave, harma dana jam’iyyar.
Alkali sai yayi tagomashin naira miliyan biyu ga dukkan kowannen da aka gurfanar gaban Shara’a, dauka kudaden wanda Abejide zai biya.
Ya kuma yi umarnin a gabtara wa lauyan Abejide kudi naira miliyan goma bisa yin biyayya wa dokar zave. Abejide dai ya garzaya kotun ne da qoqon naira ta bukatar soke batun miqawa Mark da Aregbesola shugabancin jam’iyyar ADC, da kuma kana Hukumar Zabe ta Qasa yin la’akari da ita.


