Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
Babban Hafsan Hafsoshin Sojan Kasar nan Laftanal Janar OO Oluyede ya bada tabbacin cewar a shirye dakarun sojan kasar nan suke ba dare ba rana wajen kare al’ummar kasa da diyaicin kasar nan ko ta halin kaka kuwa.
Janar Oluyede wadda Manjo Janar MS Ahmed ya wakilta ya bayyana hakan ne a yayin bikin bude wata katafariyar cibiyar karatun yara da manya da wani babban jami’in sojan kasar nan Manjo Janar Aminu Shehu Chinade ya ginawa al’ummar sa a mahaifar sa garin Chinade da ke karamar hukumar Katagum cikin Jihar Bauchi a ranar Jumu’a.
Babban Hafsan ya kara da cewar, lalle alhakin kare rayuka da dukiyar al’ummar kasar na ya ta’allaka ne ga wuyan su wadda kan hakan ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ganin sun sauke nauyin da ke ka kan su ta ko halin kaka kuwa.
Don haka ne ya roki al’ummar kasa da su ba su goyon baya don ganin sun kai ga gudanar da ayyukan su cikin nasara.
Ya kuma yabawa wannan babban jami’i na su Manjo Janar Aminu Shehu Chinade dangane da wannan aiki na taimakon jama’ar mahaifar sa da ya yi duk da cewar hukumar soja ma ta sa hannu wajen samun nasarar gudanar wannan aiki na hadin gwiwa kasancewar suna da tsari irin ya hakan wajen bada goyon baya ga duk wani babban jami’in soja mai matsayi irin na Manjo Janar Aminu Shehu Chinade wajen gudanar da ayyukan raya kasa ga al’umma.
Tun farko da ya ke jawabin makasudin wannan aiki na sa na gina katafariyar cibiyar bada Ilimi mai azuzuwa 6 da magewayi 2 da sauran su ga al’ummar sa na Chinade Manjo Janar Aminu Shehu Chinade ya ce dalilina sa shine, domin sauke nauyin da ke kan sa na bada gudummawar sa ga al’ummar sa kasancewar shi ma ai tun daga firamare har kawo ya zuwa sakandare kyauta aka ba shi Ilimi.
[28/12, 17:28] Muhammad Sani Chinade Yobe: Ya kara da cewar a yanzu kusan shekaru uku kenan ya kaddamar da wata gidauniya ta bada tallafin karatu ga dalibai wadda ya zuwa yanzu sama da dalibai 200 ne ke cin gajiyar wannan shiri na sa.
Ya kuma godewa babban hafsan tsaron kasar nan dangane da ba shi karfin gwiwar da ya yi wajen gudanar da wannan aiki kana ya kuma godewa gwamnatin Jihar Bauchi da fadar mai Martaba Sarkin Katagum da majalisar karamar hukumar Katagum dangane da ba shi goyon baya da suka yi dangane da gudanar da wannan aiki.
Kana ya godewa su ma kan su al’ummar sa na mahaifar sa garin Chinade dangane da ba shi goyon bayan da suke yi tare da fadar mai girma hakimin Chinade don ganin an kammala wannan aiki cikin nasara musamman bisa addu’o’in da suke masa.
Shi ma tun farko da ya ke jawabi mai martaba sarkin Katagum Dr Alhaji Umar Faruq Muhammad 11 wadda Ubamdoman Katagum ya wakilta godewa Manjo Janar Aminu Shehu Chinade ya yi dangane da kokarin da ya ke yiwa al’ummar sa wajen gudanar da ayyukan da ya ke yi da ya hada da gina wannan makaranta, kana ya kuma nemi sauran al’umma da ke masarautar da su yi koyi da irin wannan kokari na sa don cigaba da baiwa al’umma gudummawa musamman ma kan harkokin ilimi, samar da ayyukan yi ga matasa da makamantan su.
Da ya ke jawabi a madadin al’ummar Chinade da kuma daliban da suka amfana da wannan shiri Alhaji Sa’ad Bawa Chinade wadda tsohon babban sakataren dindindin ne a Jihar ta Bauchi ya yaba ne dangane da irin wannan kokari na Manjo Janar Aminu Shehu Chinade wadda ya mika.godiyar dukannin al’ummar garin na Chinade gare shi.
Dan majalisar dokoki mai wakiltar kasar ta Chinade da Madara a majalisar dokokin Jihar Bauchi Honarabul Nasiru Ala a cikin jawabinsa na nuna godiya ga wannan aikin taimako da Manjo Janar Aminu Shehu ya yi, ya ce tabbas janar din ya nuna shi da ne na halak domin ya yi abin da babu shi wadda suna da yakinin cewar Janar din yanzu ya fara zai ci gaba da gudanar da makamantan irin wannan aiki ga al’ummar mahaifar sa nan gaba
Ya kuma bada tabbacin cewar gwamnatin Jihar Bauchi za ta ci gaba da taimakawa wannan makaranta ta ko halin kaka don komai na tafiya dai-dai kana shi ma zai yi kokari wajen samar da masu gadi a wannan makaranta don ganin abubuwa ba su salwanta ba.
Shi ma uban wannan taro Jekada Dada Chinade ya yi matukar nuna Jin dadin sa bisa wannan gagarumin aiki da dan su Manjo Janar Aminu Shehu ya yi wadda ya masa fatan alheri tare da kalubalantar matasa ma su tasowa da su y koyi ga irin wannan hali na Janar Aminu Shehu wajen gudanar da ayyukan raya kasa ga al’ummar su.