Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiGwamnatin  Nijeriya Na Tattaunawa Da ‘Yan Kasuwa Don Karya Farashin Kayan Abinci

Gwamnatin  Nijeriya Na Tattaunawa Da ‘Yan Kasuwa Don Karya Farashin Kayan Abinci

A wani yunkuri na dakile matsalar hauhawar farashi a Nijeriya da kuma bayar da cikakkiyar kariya ga masu sayen kaya, Hukumar Kare Hakkin Masu Sayen Kaya (FCCPC), ta fara tattaunawa da masu ruwa da tsaki don warware matsalar.

Shugaban hukumar, Mista Tunji Bello a jawabin da ya gabatar gaban kungiyoyin ‘yan kasuwar da ke hada-hadar rarraba kaya a Najeriya, ya bayyana takaicinsa da yanayin yadda farashin kayan ke hauhawa ba tare da wani dalili ba, musamman kayayyakin da ake sarrafawa a cikin gida.

Matakin hukumar na zuwa a daidai lokacin da wani rahoton hukumar kididdiga ta Nijeriya (NBS), ke cewa farashin kayayyaki musamman bangaren abinci ya yi matukar hauhawa a watan Yuni da kashi 34.2 cikin 100.

Hukumar ta ce wannan adadi ya karu ne matuka daga hauhawar kashi 22.8 cikin 100 da al’umma suka gani a watan Yunin 2023.

Yanzu haka dai FCCPC na ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki daga bangarorin ‘yan kasuwa da masu hada-hadar rarraba kayaki a sassan Nijeriya.

Idan ba a manta ba, hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa baya ga yunwa su ne, suka sanya ‘yan Nijeriya fantsama titi inda suka yi zanga-zangar adawa da yanayin.

Sai dai zanga-zangar ta bar baha da kura a wasu yankuna, inda ta koma tashe-tashen hankula.

Leadership Hausa

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments