Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiShugaba Tinubu  Ya Kira Taron Hafsoshin Tsaro

Shugaba Tinubu  Ya Kira Taron Hafsoshin Tsaro

Yanzu haka Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya kulle ƙofa don  gudanar da taro da shugabannin hukumomin tsaro da a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja. Wannan taro na gaggawa, wanda aka shirya ƙarƙashin majalisar tsaro ta ƙasa ya biyo bayan ɗage taron majalisar zartarwa ta ƙasa (FEC) da aka tsara gudanarwa a yau Litinin.

Taron yana gudana ne tare da jagorancin Shugaban ma’aikatan tsaro, Janar Christopher Musa, tare da manyan shugabannin Sojoji da sauran manyan jami’an tsaro.

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, da shugaban ma’aikata na shugaban ƙasa, da Femi Gbajabiamila, da Sufeto Janar na Ƴansanda Kayode Egbetokun duk suna halartar taron.

Wannan taron dai yana gudana ne a yayin da ake ta zanga-zangar matsin rayuwa a fadin ƙasa.

Zamu kawo muku cikakken bayani nan gaba kan yadda ta wakana.

Leadership Hausa

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments