Daga, Muhammad Sani Chinade, Damaturu
Shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu ya kaddamar da tallafin noma na biliyoyin Naira ga manoman jihar Yobe da aka zabo daga mazabu kimanin 178 a jihar baki daya.
Gwamnatin jihar Yobe ce ta samar da tallafin kayayyakin aikin noman don yin alfahari da ayyukan noma da inganta samar da abinci a jihar.
Shugaban wanda mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya wakilta, ya nuna cewa noma muhimmin abu ne da ya kamata a sa himma a dukkan matakai na gwamnati “Na yi farin ciki da na shiga Yobe bisa manufar samar da abinci, kuma babu. hanyar da za mu iya cimma burinmu da manufofinmu ko a jiha ko kasa har sai mun tallafa wa manomanmu, kuma mu tabbatar da cewa sun mallaki kayan aikin na noma na zamani don inganta karfin noman su bi da bi.
A jawabinsa mai masaukin baki Gwamna Mai Mala Bunu ya bayyana cewa, shirin rabon ya kunshi manoma 30 a kowace gundumomin zabe 178 da ke jihar wanda adadin manoma 5,340 ne zasu ci gajiyar shirin.
“Sai dai tarakta guda 100 da aka samar da kuma taki duk za’a bada su ne a ofisoshin ma’aikatar noma da ke kananan hukumomin da shiyyoyin da ke jihar yayin da duk sauran kayan aikin noma da kayayyakin amfanin gona za a bayar kyauta za’a bada su ga manya da matsakaitan manoman mu da ke jihar kamar yadda aka tsara.
“A cewarsa, kokarin da muke ganin zai kara habaka ci gaban aikin noma mai yawan gaske a jihar shi ne a gaban mu.”
“Mai girma shugaban kasa a wannan karon a yau wannan aya bada baiwa ga jama’armu shiga cikin halin farin ciki da murna da dimbin jama’a tun zuwan ka, babban birnin jihar Damaturu.
“Saboda haka ina kara tabbatar muku cewa mutanen jihar Yobe nagari za su ci gaba da ba gwamnatinku goyon baya yayin da kuke kokarin inganta tattalin arziki, tsaro, da sauran kalubalen ci gaban kasa da ke addabar al’umma baki daya.
Gwamnan ya bayyana cewa “Jihar Yobe kamar yadda kuka sani na daya daga cikin jihohin da ke fama da matsalar tsaro.
“Rashin isa ga filayen noma sakamakon barazanar tsaro da sauran abubuwan da suka shafi yanayi kamar zaizayar kasa, kwararowar hamada, karancin ruwan sama da sauransu ya yi tasiri matuka ga ayyukan noma tare da samar da babban sakamako ga rayuwar al’ummarmu da suka fi yawa a fannin noma, da kuma tattalin arzikin jihar gaba daya”.
“Duk da kalubalen da ake fuskanta, aikin noma shi ne babban abin da ‘yan Yobe ke damuwa da shi lura da cewar, akasarin al’ummar Jihar manoma ne.”
Don haka, ya sanya aikin noma ya zama muhimmin fanni na shirin farfado da tattalin arzikin bayan shudewar ayyukan ‘yan tada kayar baya.
Gwamnatin jihar Yobe ta yi amfani da wadannan dabaru don farfado da fannin na noma bayan shirya muhimman taro kan harkokin aikin gona domin tsara wani sabon tsari na inganta samar da kayayyakin abinci.
Gwamnatin jihar yobe tana da kundin tsarin mulki na kwamitin gudanarwa kan farfado da aikin gona, da samar da tsare-tsare na sassan Jiha tare da hadin gwiwar gidauniyar Bill and Melinda Gates, ta samar da daftarin manufofin noma don cimma nasarar samar da abinci da bayar da gudummawa ga habaka tattalin arzikin kasa Jihar da kasa baki daya.