Gwamnan Jihar Borno a Najeriya Farfesa Babagana Umara Zulum, ya taya Hajiya Hadiza Mohammed Aliyu murnar naɗin da aka yi mata a matsayin mace ta farko da ta zama Babbar Edita (Editor-in-Chief) ta Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN).
Hadiza Aliyu, wadda ’yar asalin Jihar Borno ce, ita ce mace ta farko da za ta jagoranci sashen edita na NAN tun bayan kafuwar kamfanin sama da shekaru 40 da suka gabata.
Ta yi karatun Sadarwa da Harkokin Yaɗa Labarai (Mass Communication) a Jami’ar Maiduguri.
A cikin wata sanarwa da Mai Ba Gwamna Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai, Dauda Iliya, ya fitar, Gwamna Zulum ya bayyana Hadiza Aliyu a matsayin ƙwararriyar editan labarai, mai ladabi, jajircewa da ƙwarewa, wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aiki a NAN.
Gwamna Zulum ya ce a madadin gwamnatin da al’ummar Jihar Borno, yana taya Hadiza Mohammed Aliyu murnar wannan babban matsayi da ta samu.
Ya bayyana jin daɗinsa da labarin naɗin nata, musamman kasancewarta shugabar tawagar editoci da ’yan jaridu sama da 500 da ke aiki a ofisoshin NAN daban-daban a faɗin ƙasar da kuma yankuna 18.
Gwamnan ya kuma buƙaci sabuwar Babbar Editar ta ci gaba da kare ƙa’idojin aikin jarida da suka sanya NAN ta zama amintacciyar kafar samun labarai.
Ya ƙara jaddada mata muhimmancin ci gaba da yaƙi da labaran ƙarya, bayanan yaudara, yaɗa bayanan ƙarya da kalaman ƙiyayya, musamman yayin da ƙasar ke tunkarar lokacin yakin neman zaɓe.
Gwamna Zulum ya yi mata fatan samun nasara a wa’adinta na mulki, tare da fatan za ta jagoranci harkokin kamfanin yadda ya kamata.


