Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya amince da naɗin Alhaji Lawal Ahmed Rufa’i Safana a matsayin Mai Baiwa Gwamna Shawara na Musamman kan Sashen Binciken Harkokin Kananan Hukumomi, karkashin Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu.
Wannan naɗi wanda ya fara aiki nan take, na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka domin ƙarfafa aiwatar da ‘yancin cin gashin kai na kananan hukumomi da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ƙaddamar kwanan nan.
Zaɓin Gwamna Radda na Rufa’i ya samo asali ne daga kwarewarsa ta musamman da gwaninta a ayyukan gwamnati, musamman a fannin gudanar da harkokin kananan hukumomi, inda ya nuna ƙwarewa da gaskiya ta ban mamaki.
Wannan sabuwar kujera da aka kirkira za ta lura da yadda ake amfani da dukiyoyin gwamnati a cikin kananan hukumomi 34 na jihar, tare da tabbatar da gaskiya da rikon amana bisa manhajar “Gina Makomar Ka” da gwamnatin Radda ta kuduri aniyar aiwatarwa.
Gwamna Radda ya taya Rufa’i murna, tare da bukatar ya yi amfani da ƙwarewarsa wajen sa ido da tantance ayyuka da shirye-shiryen gwamnati domin cika alkawuran da aka ɗauka ga al’ummar jihar Katsina.
Ibrahim Kaula Mohammed
Shugaban Ma’aikatan Yada Labarai na Gwamnan Jihar Katsina
15 ga Afrilu, 2025