Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
A wani gagarumin yunkuri na maido da harkokin zirga-zirga da bunkasar tattalin arziki a yankin arewa maso gabas, hukumar raya yankin arewa maso gabas ta fara aikin gina wata muhimmiyar gada da ta hade wani bangare na jihohin Yobe da Borno.
Gadar wadda ta taso daga Katarko zuwa Gujba, Gujba zuwa Buni Yadi, sannan ta hada garin Damaturu na jihar Yobe zuwa Biu a jihar Borno, ta ruguje ne sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da aka yi a daminar shekarar ta 2024.
Aikin sake gina wannan gadar ta Katarko yana nufin farfado da haɗin kai mai mahimmanci, tallafawa ayyukan tattalin arziki, da haɓaka damar yin amfani da muhimman ayyuka a yankunan.
A kwanakin baya ne dai babban daraktan kudi da gudanarwa na hukumar, Dakta Garba Iliya, ya ziyarci wurin a madadin babban manajan darakta (MD/CEO) na hukumar NEDC, Muhammed Goni Alkali, domin duba kayayyakin gini da kuma tantance irin ci gaban da aikin ya samu don tabbatar da dorewar gadar.
Wannan yunƙuri na hukumar ta NEDC ya yi daidai da umarnin Shugaban kasa Tinubu na sake gina ababen more rayuwa da suka lalace a faɗin yankunan Jihohin arewa maso gabas.