Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, zai gina titin mota da zai ratsa shiyyoyin majalisar dattawa 3 mai tsawon kilomita 197 mai suna ‘Green Line’ ta hanyar shirin bunkasa karkara da kasuwancin aikin gona na jihar Yobe (RAAMP), domin baiwa manoma damar samun kasuwa da samar da abinci.
Kodinetan ayyukan RAAMP na jihar Yobe; Arc. Musa Suleh Damagum ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Damaturu babban birnin jihar.
A cewarsa, Gwamna Mai Mala Buni ya bayar da umarnin a yi hanyar da ta tashi daga garin Alkali a karamar hukumar Bursari zuwa Mutai na karamar hukumar Gujba, inda ta tsallaka titin gwamnatin tarayya a Ngelzarma mai tsawon kilomita 197.
“Wannan titin da ake kira ‘The Green Line’ ya ratsa dukkanin shiyyoyin majalisar dattawa uku da ke jihar, kuma zai samar wa manoma damar shiga kasuwa da kayayyakin da suke nomawa da kuma samar da abinci.
“Titin motar mai tsawon kilomita 197 da kuma wasu ayyuka da dama a jihar da gwamman ke aiwatarwa na daga cikin shirin da gwamnatinsa ta yi na samar da ababen more rayuwa na hada kowace mazaba cikin mazabu 178 da ke jihar da hanyar mota.
Ya yabawa Gwamna Mai Mala Buni bisa jajircewar sa wajen sanya jihar Yobe a matsayin daya daga cikin Jihohin da ke da kudirin aiwatar da wannan shiri na RAAMP wanda ya mayar da hankali wajen bunkasa karkara da habaka noma.
Musa Damagum ya jaddada cewa, a karkashin jagorancin Gwamna, an tsara aikin ne domin kara inganta gine-gine da gyaran manyan titunan karkara, da tabbatar da shiga kasuwanni ga manoma ba tare da wata matsala ba, tare da bayar da tallafi mai muhimmanci domin daukaka rayuwar al’ummar karkara.
Da yake bayyana kwarin gwiwa ga kudirin Gwamnan na cika alkawuransa, Arc. Musa Damagum ya bada tabbacin cewa jihar Yobe na gab da samun sauyi na cigaban yankunan karkara da kuma bunkasar al’umma.
Ya nanata cewa gwamna Buni ya jajirce wajen ganin ya magance bukatu na musamman na al’ummomin karkara yadda zai haifar da ci gaba mai inganci mai dorewa a fadin jihar.