Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu
Hukumar alhazai ta jihar Yobe ta gudanar da wani muhimmin taro karkashin jagorancin shugaban hukumar Alhaji Mai Aliyu Usman kan yadda za’a tsara shirye-shiryen hajiin bana daga nan gida Najeriya kaiwa ga kasa mai tsari ya Saudi Arabia
A yayin taron shugaban hukumar ya yi wa mambobin kwamitin alhazan karin haske kan tsare-tsaren da aka yi don samun nasarar daidaitawa da jin dadin alhazan da ke shirin gudanar da aikin Hajji na shekarar 2025.
Mai Aliyu ya ce, tuni gwamnatin jihar ta samar da duk wasu muhimman kayayyaki don saukaka tafiyar mahajjata, wadanda suka hada da jakunkuna, kayan sawa na maza da mata, da kuma lambar tantancewa.
Wannan tallafi mai fa’ida yana nuna Æ™udurin gwamnati na tabbatar da kwanciyar hankali, aminci, da daidaita aikin hajji na bana 2025.
Ya jaddada kudirin hukumar na ganin an gudanar da aikin hajji cikin kwanciyar hankali da lumana ga dukkan maniyyatan jihar Yobe.
A yayin taron, shugaban hukumar, tare da mambobin kwamitin Hajji, sun karbi allurar rigakafin da ma’aikatan aikin hajji suka gudanar.
Wannan ya nuna yadda aka fara shirye-shiryen aikin hajji na shekarar 2025, tare da tabbatar da lafiya da amincin dukkan jami’ai da maniyyata.
Wadanda suka halarci taron sun hada da Amirul Hajj, mai martaba Alhaji Abubakar Muhammad Ibn Grema (Mai Tikau), da Mohammed Mairami, a matsayin sakataren kwamitin, Alhaji Gana Fantami, dan kwamitin, Sanata Alkali Jajere, memba sai mai shari’a Uwani, memba da sauran mambobin kwamitocin aikin hajji.
Taron ya kuma kasance wani dandali ga mambobin kwamitin don yin shawarwari kan muhimman dabaru da kuma fahimtar yadda za’a samu gudanar da ingantaccen aikin hajji.