A wani lamari mai cike da ruɗani, fitaccen shugaban ƴan bindiga da ake tsoro a jihar Katsina, Kachalla Harisu, ya gamu da ajalinsa tare da wasu ƴan tawagarsa goma, bayan rikicin cikin gida da ya barke tsakanin ɓangarori biyu na ƴan bindiga a dazukan da ke tsakanin ƙananan hukumomin Safana da Dutsin-Ma.
Majiyoyin sirri sun shaida wa Zagazola Makama cewa rikicin ya faru da sanyin safiyar Talata, sakamakon sabani kan rabon kuɗin fansa da iko da yankunan da ke ƙarƙashin ɓangarorin biyu.
“Kachalla Harisu da tawagarsa sun shiga sabani da wata ƙungiya ta daban dangane da rabon kuɗin fansa da shugabanci. Cece-kuce ya rikide zuwa harbe-harbe, wanda ya yi sanadin mutuwar Harisu da mutane goma daga cikin magoya bayansa,” in ji wata majiya.
Marigayin Kachalla Harisu ya daɗe yana neman ruwa a jallo daga hukumomin tsaro, saboda zargin hannu cikin hare-hare masu kisa, garkuwa da mutane da satar shanu a sassa daban-daban na Katsina da Zamfara.
Masana tsaro na kallon wannan rikici a matsayin alamar raguwar haɗin kai tsakanin ɓangarorin ƴan ta’adda, tare da bayyana hakan a matsayin damar sauƙa ga al’umma da ke fama da azabar hare-haren dajin.
Daga Zagazola Makama