Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiGwamna Buni Ya Samar Da Hanyoyi A Garuruwan Tagali, Masaba Da Karasuwa-Galu

Gwamna Buni Ya Samar Da Hanyoyi A Garuruwan Tagali, Masaba Da Karasuwa-Galu

Na tsawon shekaru aru-aru, al’ummomin Tagali, Masaba da Karasuwa-Galu da ke fama da matsalolin hanyoyi saboda ambaliya da ruwa, sun dade suna rokon gwamnati da a gina musu hanya da za ta hada su da sauran sassan duniya – amma sai yanzu aka cika wannan buri.

A wata sanarwa daga Mamman Mohammed, Daraktan Yada Labarai da Harkokin Watsa Labarai na Gwamnan Yobe, ya bayyana cewa wasu daga cikin waɗanda suka fara wannan yaki sun rasu ba tare da ganin burinsu ya cika ba, wasu kuma sun daina fatan ganin hanyar, sai dai zuwan Gwamna Mai Mala Buni ya kawo sauyi ta hanyar bayar da kwangilar gina hanyoyin.

Tun kimanin shekaru 52 da suka gabata, lokacin da ake gina titin tarayya na Gashua-Nguru a lokacin tsohuwar jihar Arewa Maso Gabas, al’ummar Karasuwa-Galu sun nemi a karkata hanyar zuwa garinsu, amma hakan bai samu ba.

Sun ci gaba da fatan ganin hanyar daga lokacin tsohuwar jihar Borno, har zuwa shekaru 32 da kafuwar jihar Yobe, amma ba a aiwatar ba sai zuwan wannan gwamnati.

Haka kuma, hanyar Chumbusko zuwa Tagali ta kasance ba ta da amfani ga ababen hawa tsawon shekaru, lamarin da ya yi wa Tagali tarnaki wajen samun cigaban da ya kamata, musamman a lokacin damina.

Al’ummar Masaba ma sun sha wahala iri ɗaya, inda wahalar kai kayayyaki da marasa lafiya zuwa asibitin Gashua ta zama ruwan dare.

Da dama daga cikin waɗanda suka fara wannan fafutukar ba su samu damar rayuwa su ga lokacin da Gwamna Buni ya kawo mafita ba.

A shekarar 2023, gwamnatin jihar Yobe ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamna Mai Mala Buni, CON, COMN, ta fara aikin gina hanyoyin domin kawo karshen wahalar da al’ummomin suka sha.

Abin farin ciki ne cewa gwamnatin jihar ta sake gina tsohuwar hanyar Danchua-Jajere, wanda hakan ya farfado da walwala da tattalin arzikin yankin.

Yayin da wasu daga cikin hanyoyin aka riga aka kammala, wasu kuma suna dab da gamawa, rayuwar tattalin arziki a garuruwan da suka ci gajiyar aikin ta karu sosai, wanda ya kawo ayyukan yi da yawaitar arziki.

Hanyoyin da aka gina sun kuma rage damfarar da masu siye da siyarwa (dillalai) ke yi wa manoma, wanda yanzu suna iya kai kayayyakinsu zuwa kasuwannin Gashua da Nguru cikin sauki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments