Sunday, April 27, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiAn Horar Da  ‘Yan Jarida Da Jami’an Tsaro A Kebbi

An Horar Da  ‘Yan Jarida Da Jami’an Tsaro A Kebbi

Wata ƙungiya mai zaman kanta (Search for Common Ground) da ke aiki wajen samar da zaman lafiya da warware rikice-rikice, ta fara wani shirin horo ga ‘yan jarida da jami’an tsaro a Birnin Kebbi.

Shirin, wanda ke da nufin ƙarfafa haɗin gwiwa domin samar da zaman lafiya da tsaro a ƙauyukan kan iyakar Najeriya da Binin, ya shafi jihohi biyar – Kebbi, Katsina, Zamfara, Kwara da Neja.

‘Yan jarida da jami’an tsaro da aka zaɓo daga jihohin biyar suna halarci horon da ake gudanarwa a Azbir Hotel da Rayhaan University da ke Birnin Kebbi.

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na Jihar Kebbi, Alhaji Yakubu Ahmed BK, wanda ya gabatar da jawabin bude taron, ya bayyana yadda Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, tun bayan hawansa kan karagar mulki shekaru biyu da suka wuce, ya fuskanci matsalar ‘yan bindiga a kudancin jihar – inda matsalar ta hana manoma shiga gonakinsu.

Ya ce, matakin haɗa kai da jami’an tsaro a matakin koli da kuma ingancin matakan da aka ɗauka sun nuna tasiri matuƙa wajen magance matsalar, wanda hakan ya kai ga samun zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.

Kwamishinan ya ƙara da cewa dimbin amfanin da aka samu a daminar da ta gabata hujja ce ta cewa matakan sun yi tasiri. Ya kuma bayyana fatan cewa daminar da ke tafe za ta kasance mai albarka kamar ta baya.

Ya bayyana horon da ake gudanarwa a matsayin mai muhimmanci kuma daidai lokacin da ake buƙata, tare da jaddada kudurin gwamnatin Kebbi na ci gaba da ƙarfafa zaman lafiya a dukkan sassan jihar ta hanyar ƙarfafa haɗin kai tsakanin jami’an tsaro da al’umma, ba kawai a kan iyaka ba har ma a fadin jihar.

Ya yi maraba da ‘yan jarida da jami’an tsaro da suka fito daga jihohin da shirin ya shafa zuwa Jihar Kebbi, tare da gayyatar su zuwa wani zagayen ziyara domin kallon wasu manyan ayyukan ci gaba da gwamnatin Dakta Idris ta aiwatar cikin shekara biyu kacal.

Shirin horon dai zai ci gaba har zuwa ranar Alhamis.

Ahmad Hussaini Aliyu, Mai Taimakawa Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na Jihar Kebbi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments