Daga Imrana Abdullahi
An yi kira ga Gwamnatoci a matakai gida uku na Najeriya da sauran manoma masu hannu da shuni da su mayar da hankali wajen shuka itacen Dabino domin muhimmancinsa da ya hada da magance yunwa da sauran albarkatun ci gaban tattalin arziki da yawa.
Dokta Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ne ya yi wannan kiran a lokacin gabatar da wa’azin watan Ramadana da yake gudanarwa a masallacin Sultan bello Kaduna.
Dokta Gumi ya ci gaba da bayanin cewa muhimmanci da albarkar da ke cikin itacen dabino hakika ya na da yawan gaske fa har ya wuce a yi misalinsa a dan kan kanin lokaci.
“Kamar yadda Annabi Mihammadu SAW ya yi bayanin cewa da za a yi tashin alkiyama amma sai ya kasance a hannun mutum akwai jaririn itacen dabino, manzon Allah ya ce to, ka Dasa shi wato mitum ya shuka shi domin akwai alkairi kwarai a cikin lamarin”.
“Ko a lokacin shugaban Saudiyya marigayi Faisal cewa ya yi idan turawa sun matsa masu zai katse mI sannan idan ma ba man za su koma rayuwa da dabino da sauran wasu itatuwa kamar yadda iyayensu da kakanni suka rayuwa tun can baya.
Dokta Gumi ya kuma yi kira ga daukacin al’immar Najeriya da su tashi tsaye wajen gyaran makarantu tun daga kasa zuwa can sama wato jami’o’i.
Saboda mu dadin da muka ji lokacin da muka yi karatun jami’a a jami’ar Ahmadu Bello Zariya (ABU) ko a makarantun kasadhen waje a lokacin ba a samun irin wannan dadin da kula wa ga dalibai domin za a yi mana wanki kuma mu da muke yin katatun likita ana ba mu kudin alawus din da ya isa mutum ya sayi mota a wancan lokaci Amma yanzu fa, don haka dole tashi tsaye gyara makarantu”.
Ya kuma yi kira ga iyaye da su daina kiyawa yauansu karya domin idan ka ce wa yaron ka idan anzo nema na ka ce ba na nan hakika ka koya wa yaro karya don haka a kiyaye a kuma daina.