Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiZamu Dauki Matakin Doka Kan Duk Wanda aka Kama da Laifi –...

Zamu Dauki Matakin Doka Kan Duk Wanda aka Kama da Laifi – Inji Dr. Kamaluddeen Bashir 

Daga Sa’id Surajo

Gwamnan Malam Dikko Umar Radda, ya kaddamar da Kwamitin Mazabu na Shirin Cigaban Al’ummah a Jihar Katsina a Shiyyar Daura.

Gwamnan ya samu wakilcin kwamishinoni da masu ba gwamna shawara a karkashin jagorancin kwamishinan kudi na Jihar Katsina, Dr. Bishir Tanimu, domin kaddamar da kwamitocin a harabar sakatariyar karamar hukumar Daura.

Kwamitin Cigaban Al’ummah na Jihar Katsina, na daga cikin sabbin tsare-tsaren gwamnatin Dikko Radda domin inganta rayuwar al’ummah da yankunansu.

A karkashin wannan shirin, za a kafa kwamitin amintattu na mutane goma daga kowace mazaba, wanda zai hada da iyayen kasa, malamai, ma’aikatan gwamnati, da shugabanni.

Wannan kwamiti zai rika gano bukatun al’ummar mazabar tare da isar da su ga babban kwamiti.

Daga bisani, babban kwamitin ne zai amince da fitar da kudade domin aiwatar da ayyukan ci gaba.

Da yake jawabi, Shugaban Shirin na Jihar Katsina, Dr. Kamaluddeen Kabir Katsina , ya bayyana cewa an tanadi dokokin da za su hukunta duk wani mamban kwamiti da aka samu da aikata rashin gaskiya ko cin amanar wannan shirin.

 

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments