Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya dage dakatarwar da aka yiwa shugaban karamar hukumar Machina Hon. Idrissa Alhaji Bukar Machina a kwanakin baya sakamakon rashin biyayya da Kuma da’ a da ake zargin sa da yi.
Hakan na kunshe ne cikin wata takardar sanarwa mai dauke da sa hannun Alhaji Shuaibu Abdullahi, sakataren yada labaran Sakataren gwamnatin jihar, wacce aka rabawa manema labarai a Damaturu.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, an dage dakatarwar ne bisa rubuta nadama sa da yayi a rubuce wadda hakan ya nuna ba zai sake aikata abin da ake zargin sa da yi ba nan gaba wadda ya haifar da dakatar da shi da Gwamnan ya yi.
“Kafin sake mayar da shi kan kujerar jagorancin karamar hukumar sai da aka tattaunawa da ma’aikatan kananan hukumomin da Kuma dukannin masu ruwa da tsaki domin ci gaban karamar hukumar Machina da jihar Yobe baki daya.”