Daga Rabiu Sanusi
Shugaban Kwamitin Kula da Binciken kadarori da aka kafa a Karamar Hukumar Ungogo, Dr. Saminu Umar Rijiyar Zaki, ya kammala aikinsa yakuma gabatar da rahoton ga shugaban riko na karamar hukumar ungogo Alh sani Abdu ungogo a ofishinsa.
Wannan na zuwa ne a wata sanarwa da Mai magana da yawun Karamar Hukumar ya fitar ga manema Labarai
Rahoton, wanda ya ƙunshi ayyuka, ci gaba, da ƙalubalen da karamar hukumar ta fuskanta yayin lokacin canjin shugabanci,
Dr. Saminu Umar ya nuna godiya bisa damar da aka ba shi na jagoranci tare da jaddada manyan bangarori da za a mayar da hankali kansu a lokacin shugabancinsa, ciki har da ci gaban ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, da haÉ—in kai da al’umma.
Jami’in rikon na karamar hukumar ungogo Alh sani Abdu bayan karÉ“ar rahoton, ya yabawa Dr. Saminu Umar da dukkan kwamitin kula da canji bisa Æ™wazo da jajircewarsu.
Ya kuma kara da cewa za a binciki aiyyukan kwamitin da yakawo tare da shawarwari da suka bayar.