Bello Galadanchi, sanannen matashi ne mai wayar da kan jama’a akan al’amurran Gwamnati da masu mulki a dukkan matakai.
Bello Galadanchi da aka fi sani da Dan Bello, yana gabatar da bidiyoyin wayar da kan al’umma ne ta hanyar Kafar Sadarwa ta Zamani.
A dai-dai lokacinda aka tunkari gudanar da zanga-zangar game gari da aka yi a fadin kasar nan, Dan Bello ya fitar da bidiyoyi kala-kala da suka shafi batutuwa daban-daban akan zanga-zangar.
Daga cikin irin wadannan bidiyoyi, akwai wanda Dan Bello ya fitar akan zargin cewa an baiwa Malaman Addini kudi domin su hana zanga-zanga.
Sai dai, duk da wannan zargi da ya yi na cewa an baiwa Malaman naira Miliyan 16 kowannen su, har a halinda ake ciki babu tabbacin hakan.
Bayan wannan zargi da Dan Bello ya yi, sanannen Malamin Addinin Islama Sheikh Yakubu Musa Hassan, ya fito ya magantu akan wannan zargi.
Sheikh Yakubu Musa Hassan ya musanta wannan zargi na Dan Bello, inda ya ce duk wanda ya san an basu kudi akan wannan batu to suna mika koken su ga ubangiji akan ya bi masu hakkin su, domin ko sisin Kobo ba’a basu ba.
To kenan idan har malami mai kima irin Sheikh Yakubu Musa zai fito ya bayyana hakan, akwai yiyuwar akwai lauje cikin nadi a zargin da Dan Bello ya yi na baiwa malaman kudi.
To anan yana da kyau al’umma su gane cewa Dan Bello fa Allan Misra ba ne, duk bidiyon da ya fitar zargi ne, ba wai yana nufin da gaske ba ne duk abinda ya fada.
A sabili da irin wadannan bidiyoyi na Dan Bello, ko a kwanannan wasu yan Najeriya sun fara kiraye-kiraye akan Hukumomi su kama tare da hukunta shi akan irin wadannan bidiyoyi da yake fitar wa na zargin shuwagabanni ba tare da cikakkar hujja ba, wanda hakan ka iya tunzura al’ummar Najeriya.