Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya gwangwaje kungiyar kwallon kafa ta El-Kanemi Warriors da kyautar kudi har Naira miliyan 35.2 saboda rawar da suka taka a gasar cin kofin shugaban kasa na 2024 da suka yi.
Nasarar da kungiyar ta samu a kan Abia Warriors da ci 2-0 a wasan karshe ya kawo karshen tsawon lokacin da aka shafe kusan shekaru 32 da kungiyar ta El-kanemi ta shafe ba tare da lashe wannan gasa ba sai a bana.
Dangane da nasarorin da suka samu, kowane dan wasan da ke cikin kungiyar da ta yi nasara ya samu alawus din kudi har Naira miliyan daya.
Sakataren gwamnatin jihar Bukar Tijjani ne ya gabatar da kudin a madadin gwamnan a sakatariyar Musa Usman dake Maiduguri.
Baya ga kyautar da gwamnatin jihar ta yi, an kuma ba kungiyar kyautar kudi naira miliyan 50 saboda nasarar da suka samu na kashe wannan gasa.
Kwamishinan Wasanni Kwamared Saina Buba, ya nuna jin dadinsa ga Gwamna Zulum sakamakon nadin da ya yiwa Babagana Kalli a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin wasanni.
Mai baiwa El-Kanemi Warriors shawara a fannin fasahar taka leda, Aliyu Zubairu, ya yabawa kokarin gwamnatin jihar wajen inganta harkokin wasanni amma ya yi kira da a fitar da kudade a kan lokaci domin saukaka alkawurran tafiye-tafiyen kungiyar.
Wannan Nasarar da kungiyar ta El-kanemi ta samu al’ummar Jihar ta Borno sun nuna matukar farin cikin su akai wadda ake kallon wannan kyauta da Gwamnnan ya ba su a matsayin tukuicin sakamakon wannan gagarumin ci gaba da harkokin wasanni ya samu a yankin na Borno.