…..Tsagin Mustapha Inuwa Ya Maka Tsagin Yakubu Lado Kotu
Ko me ya sanya tsagin Dr Mustapha Inuwa suka kaurace wa shiga zaben shuwagabannin jam’iyyar PDP na jihar Katsina?.
A ranar Asabar 10 ga watan Ogusta na shekarar 2024, Uwar Jam’iyyar PDP ta jihar Katsina ta gudanar da zaben shuwagabannin jam’iyyar PDP a matakin Kananan Hukumomi 34 da ke Jihar.
Haka kuma a sati biyun da suka gabata, Uwar Jam’iyyar ta jihar Katsina ta kuma gudanar zaben Shuwagabanni a matakin Mazaɓu.
Sai dai a dukkanin zabukan babu mutanen tsagin tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina Dr Mustapha Muhammad Inuwa, sai dai mutanen Sanata Danmarke.
A wani rohoto da Katsina Daily News ta samu ya nuna cewa,tsagin na Dr Mustapha Inuwa sun ce sun kai kara kotu sakamakon rashin basu dama su shiga zaben kamar yadda Kudin Jam’iyyar ya tanada, amma aka tauye masu wannan haƙƙin.
Kamar yadda ya zanta da manema labarai a yau Asabar Arc. Ahmed Aminu Yar’Adua wanda daya ne daga cikin tsagin Dr Mustapha Inuwa,ya ce Uwar Jam’iyyar a Jiha ta ki ta sayar wa mutanen su fom din shiga takarar.
“Duk da cewa mun ware kudinmu sama da Naira miliyan N97m don siya wa mutum sama da 7,000 da suka cancanci shiga zaben amma aka ki sayar mana da fom din”
Ya kuma ce sun garzaya har Shalkwtawar Jam’iyyar da ke Abuja don bayyana masu abin da ke faruwa amma ba wani matakin da aka ɗauka, shi ya sa suka kai kara kotu, kuma maganar na gaban kotu.
Ana sa ran ranar Litinin din nan mai zuwa za ta yi hukunci.
Sai dai a bangaren uwar jam’iyyar PDP da ke Katsina,ta musunta dukkanin zarge-zargen nasu, sannan ta ce har yanzu babu wani umurnin kotu da aka aiko masu wanda ya hana a gundumar da zabe.
Mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na shiyar Katsina dake riko a yanzun Tijjani Umar ya ce jam’iyyar ba ta sami wata takarda daga kotu ba da za ta hana ta gudanar da zaɓe.