Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi, ya yi sanadiyar rushe wata karamar gada da ke gab da garin Buskuri kilomita 13 tsakanin sa da garin Azare a jihar Bauchi da ke kan hanyar Kano zuwa Maiduguri, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin sufuri tsakanin jihohin yankin arewa maso gabas da suka hada da Yobe, Taraba, Adamawa, Gombe, Borno, da makwaftan Kasashen Nijar, Chadi, Kamaru da sauran kasashen Afirka ta tsakiya.
Wani ganau da ke garin na Buskuri ya bayyana wa wakilin mu cewar, wannan ruwan sama an dauki sa’o’i ana shekaru shi kamar da bakin kwarya wadda saboda tsakanin yawan sa da yadda ya ke zuwa da karfi shi ya haddasa share wannan karamar gada tare da rushe dukan hanyoyin biyu hade da gonaken da ke gab da yankin.
Ya Kara da cewar, lokacin da suka ga wannan ruwan sama ya karya wannan karamar gada hankalin su ya tashi domin sun ji tsoron kar ruwan ya shigo garin su amma cikin rahamar Ubangiji Allah SWT ruwan ya fada daji.
Don haka ana ba masu ababen hawa da matafiya shawara sosai da su tuntubi kungiyoyin sufuri don ƙarin bayani kan amincin hanya kafin shirya tafiye-tafiyensu.
An yi kira ga gwamnatocin jihohi a yankunan da abin ya shafa da su aiwatar da dabarun tsugunar da mazauna kusa da gabar kogi zuwa wurare masu aminci don dakile illolin da ke tattare da ci gaba da afkuwar ambaliyar ruwa a wadannan yankuna lura da cewar, da ma a baya hukumar kula da yanayi ta kasa ta yi hasashen samun ambaliyar ruwa a yankuna da dama na kasar nan.
Wannan yankewar gada ya tilasa ma.su ababen hawa da ke bin hanyar daga Borno, Yobe, Gombe da Adamawa ala tilas sai sun zaga ta garuruwan Bulkachuwa, Chinade, Hardawa, Misau da Zadawa kafin su Isa garin Azare yadda za su kama hanyar zuwa Kano.