Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiAn Kashe Manoma 8 Da Sace Dabbobi 1,260 A Sakkwato

An Kashe Manoma 8 Da Sace Dabbobi 1,260 A Sakkwato

‘Yan bindiga daga Mali sun kashe Manoma takwas tare da kwashe dabbobi 1,260 a yankin Karamar Hukumar Gudu ta Jihar Sokoto. ‘Yan bindigar, wadanda suka shigo Nijeriya daga Mali, sun sace shanu 260 da tumaki da awaki 1,000 daga al’ummomin yankin.

A cewar Alhaji Umar Maikano Balle, Shugaban Karamar Hukumar Gudu, ‘yan bindigar sun yi kokarin lalata bututun mai a Jamhuriyar Nijar amma jami’an tsaro na Nijar suka hana su, wanda hakan ya sa suka kai hari kan manoman.

Balle ya bayyana cewa jami’an tsaro sun samu labarin ‘yan bindigar suna cikin wani daji a Gudu. Duk da kokarin fatattakar ‘yan bindigar, ruwan sama mai yawa kamar da bakin kwarya ya hana motar jami’an tsaro kai dauki, wanda ya bai wa yan bindigar damar tserewa. Maharan sun kuma kai hari a kauyen Karfen Sarki, inda suka kashe manoma takwas, ciki har da mambobi biyar na tsaron al’umma a Sokoto da mazauna kauyen uku.

Wannan ba shi ne karo na farko da irin wannan harin ke faruwa ba, domin yan bindiga daga Mali sun sha kai hari a baya. Balle ya jaddada barazanar da wadannan ‘yan bindiga ke yi, wadanda ke amfani da iyakar da ke tsakanin Nijar da Nijeriya wajen satar dabbobi da tayar da hankalin al’umma.

Leadership Hausa

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments