Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeTsaroZanga-zanga: 'Yan Sanda Sun Tsare Wasu Mutane 90 Da Ake Zargi Da...

Zanga-zanga: ‘Yan Sanda Sun Tsare Wasu Mutane 90 Da Ake Zargi Da Wawure Dukiyar Jama’a A Yobe

Daga, Muhammad Sani Chinade, Damaturu

Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta ce ta kama wasu mutane 90 da ake zargi da hannu a zanga-zangar da aka yi ranar Alhamis a jihar wadda ya Kai ga barnata kayan jama’a a wasu garuruwan Yobe.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Dungus Abdulkarim, ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Damaturu, inda ya ce adadin wadanda ake zargin kawo yanzu sun koma 108.

DSP Dungus  ya ce an tsare wadanda ake zargin ne a garuruwan Nguru, Potiskum da Gashuwa.

A cewarsa, an kama su ne da laifin wawure dukiyar jama’a, da kuma karya dokar hana fita a yankunan da lamarin ya shafa da dai sauransu.

Ya bayyana cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu idan an kammala bincike akan su.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya yi kira ga jama’a da su kai rahoton duk wanda aka gani da dukiyar sata domin gurfanar da su gaban kuliya.

Abdulkarim ya bayyana cewa an dawo da zaman lafiya a yankunan da lamarin ya shafa bayan da aka tura ‘yan sanda da yawa.

Ya ce kwamishinan ‘yan sanda a jihar, CP Garba Ahmed, ya bukaci masu zanga-zangar da su shiga tattaunawa da gwamnati domin biyan bukatunsu maimakon tayar da hankali.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments