Daga Muhammad Sani Chinade, Damaturu
Bayan da aka samu ci gaba a harkar tsaro a garuruwan Potiskum, Gashua da Nguru, Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni ya amince da sake duba dokar hana walwala da aka sa musu tun ranar farko sakamakon ‘yar hatsaniya da aka samu a cikin zanga-zangar da matasan su ka fara gudanarwa da sa’o’i biyar.
A cikin wata sanarwa da Birg Dahiru Abdulsalam (Rtd) mai bada shawara kan harkokin tsaro ga Gwamna Buni ya ce, yanzu an sassauta dokar hana fita daga karfe 12:00 na rana zuwa 5:00 na yamma domin mutane su gudanar da ayyukan su daga ranar Lahadi 4 ga Agusta 2024 har zuwa lokacin da komai zai komai kamar yadda ya ke a baya.
Kan haka ne ake umurci hukumomin tsaro da su kula da matakin da ake ciki a yanzu don tabbatar da cewa wasu batagari ba su amfani da wannan dama ba don cimma munanan manufofin su da zai haifar da rashin bin doka da oda.
Don haka, ana buƙatar ‘yan ƙasa masu bin doka da su aiwatar da nasu ayyuka na halal a lokacin wannan doka da zata rika farawa daga karfe 12:00 na rana zuwa karfe 5:00 na yamma kowace rana.
Gwamnan na rokon al’umma su cigaba da addu’ar neman zaman lafiya mai daurewa a dukkan Jihar da ma kasa baki daya.