Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiZanga-zanga: Gwamna Buni Ya Yabawa Matasan Yobe Kan watsi Da Suka Yi...

Zanga-zanga: Gwamna Buni Ya Yabawa Matasan Yobe Kan watsi Da Suka Yi Da Shiga Zanga-zanga 

Daga, Muhammad Sani Chinade, Damaturu

Gwamnan jihar Yobe,  Mai Mala Buni CON, ya yabawa al’ummar jihar musamman matasa bisa yadda suka aminta da kiraye-kirayen da ake yi na kin amincewa da zanga-zangar a daidai lokacin da jihar ke fitowa daga kalubalen tsaro da ta dade tana fuskanta.

A wata sanarwa da ke dauke da sa hannun babban Darakta kan  harkokin yada labarai na Gwamna Buni, Mamman Muhammad ya raba wa manema labarai a garin Damaturu, ya bayyana cewar, Gwamnan ya ambata cewar,  “Ina nuna farin ciki na a kan sanin  halin da muka fito ciki da matasan jihar suka yi  daga halin da jihar ta shiga na rikicin masu tada kayar baya na tsawon lokaci wadda suka amsa kiran da muka musu na kin shiga zanga-zanga.”

“Al’ummar Yobe musamman ma matasanmu masu kishin kasa sun nuna kauna, damuwa da kishin kasa ga jihar ta hanyar bin kiraye-kirayen kin shiga zanga-zangar,” inji shi.

Gwamnan ya ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta fadada manufofinta da shirye-shiryenta don inganta farfadowa da bunkasar tattalin arziki, da kuma tabbatar da dimbin masu cin gajiyar shirye-shiryen sun yawaita.

“Kwanan nan mun kaddamar da gagarumin shirin karfafa aikin noma domin bunkasa shi don  tabbatar da wadatar abinci da tsaro a jihar.”

“Kamar yadda kuka sani manoma 20 daga kowace mazaba cikin mazabu 178 na siyasa da Jihar ke da shi suna cin gajiyar shirin karfafa aikin na gona, baya ga samar da ayyukan yi ga matasanmu da gwamnatin ke yi a dukkan sassan mazabun Jihar.”

Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnati za ta tabbatar da cewa jihar Yobe ta zama abin koyi a fannin noman damina da na rani.

Gwamnan ya kuma kara ba da tabbacin cewa, da irin wannan fahimtar gwamnati za ta ci gaba da aiwatar da manufofi da tsare-tsare masu dacewa da jama’a don inganta rayuwar al’umma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments