Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Nasser Kanani, ya mika sakon ta’aziyya kan mutuwar shugaban Hamas, Ismail Haniyeh, inda ya bayyana shi a matsayin cin zarafi.
A cewar shafin Intanet na ma’aikatar, Kanani ya bayyana cewa za su dauki fansa kan kisan da aka yi wa Haniyeh.
Ya ce Iran tana gudanar da bincike amma mutuwarsa za ta kara karfafa dangantaka tsakanin Iran da Falasdinawa.
Idan ba a manta ba da safiyar ranar Laraba ne, kungiyar Hamas ta ce an kashe shugabanta, Ismail Haniyeh a birnin Tehran na Iran.
Wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ce an kashe Haniyeh ne a gidansa da ke Tehran, a ziyarar da ya kai domin halartar bikin rantsar da sabon shugaban Iran, Masoud Pezeshkian.
Kungiyar Falasdinawan mai rike da iko a Gaza ta ce Isra’ila ce ta kashe shugaban nata, m yayin da yake halartar rantsar da sabon shugaban Iran.
Kungiyar Hamas ta bayyana kisan a matsayin babban laifi wanda martaninsa ba zai zo da dadi ba.
Ta kuma ce Isra’ilan ta kashe daya daga cikin masu tsaron lafiyar Haniyeh, a lokacin samamen da ta kai.
Leadership Hausa