Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiMalamin Addinin Islama A Yobe  Ya Bukaci Matasa Da Su Gujewa Zanga-zangar...

Malamin Addinin Islama A Yobe  Ya Bukaci Matasa Da Su Gujewa Zanga-zangar Da Suka Shirya Yi Saboda Gudun Abin Da Za Ta Haifar

Daga, Muhammad Sani  Chinade, Damaturu

Wani Malamin addinin Musulunci na Yobe Ustaz Babagana Mallam Kyeri ya yi kira ga al’umma musamman matasa da su guji shiga zanga-zangar da suka Shirya  yi a fadin kasar nan daga gobe 1 ga watan Agusta zuwa 10 ga Agusta, 2024 lura da cewar ba’a san abin da za ta haifar ba.

A jawabinsa a Damaturu babban birnin jihar Yobe,  Malamin addinin Islaman  ya amince da kalubalen tattalin arzikin da talakawan Najeriya ke fuskanta, yana mai bayyana su a matsayin na wucin gadi in Allah ya so sauki na zuwa nan gaba.

Ya kuma jaddada muhimmancin yin hulda da gwamnati ta hanyar tattaunawa maimakon yin zanga-zanga, wanda ya yi gargadin cewa masu tayar da kayar baya za su iya amfani da su wajen haifar da mummunan sakamako ba fata ba.

Malamin ya Kara bayyana munanan sakamakon da aka samu a wasu kasashen da suka fito daga irin wannan zanga-zangar da kuma abubuwan da suka faru a baya-bayan nan game da zanga-zangar da wata kungiya ta aiwatar  a shekarun baya a Najeriya wadda ‘yan ta’addan cikin su suka rika barnata kayayyakin mutane da na gwamnati haka siddan.

Babagana Malam Kyari wanda shi ne mashawarci na musamman ga Gwamna Mai Mala Buni kan harkokin addini ya jaddada muhimmancin tunkarar kalubale tare da kyakkyawar tunani da dabaru, inda ya bukaci shugabannin wannan zanga-zangar da su yi la’akari da matakin da suka dauka don kaucewa jefa kasar nan da al’ummar ta cikin mummunan hali.

Malamin addinin Islama ya ba da shawarar a guji yin gaggawar daukar mataki wadda bacin  rai ke haifarwa, yana mai bayar da shawarar yin nazari sosai kan lamarin kafin daukar kowane mataki.

Masanin ya kirayi  matasan da su yi tunani mai zurfi da kuma neman mafita mai ma’ana don magance matsalolin al’umma, inganta haɗin kai a tsakanin mahalarta wannan zanga-zangar  yadda ya kamata ba tare da yin rikici ba matukar sun tubure akan sai sun yi.

Malam Kyari ya jaddada muhimmancin hakuri da kuma ci gaba a sannu a hankali wajen samar da sauyi, inda ya bukaci daidaikun mutane da su ci gaba da jajircewa wajen yin shawarwari cikin lumana da inganci a matsayin mabudin warware matsalolin da kuma ci gaba mai inganci a ko ina a duniya.

Malamin na Islama ya yiwa kasar nan da al’ummar ta fatan alheri da kuma addu’ar Allah SWT ya kare mu daga fadawa sharrin makiyan kasar mu daga cikin gida da wajen ta.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments