Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeTsaroSufeton ‘Yansanda Ya Gindaya Sharadi Ga Masu Zanga-zangar Matsin Rayuwa

Sufeton ‘Yansanda Ya Gindaya Sharadi Ga Masu Zanga-zangar Matsin Rayuwa

Sufeto Janar na ‘yansanda, Kayode Egbetokun, ya buƙaci dukkanin ƙungiyoyin da ke shirin gudanar da zanga-zangar a faɗin ƙasar nan da su miƙa bayanansu ga kwamishinonin ‘yansanda a jihohinsu.

Egbetokun, wanda ya zanta da manema labarai a shalkwatar rundunar ya ce an gabatar da buƙatar ne don ganin an gudanar da zanga-zangar cikin lumana tare da bayyana cewa bayanan sirri da rundunar ta samu sun nuna cewa sojojin haya na ƙasashen waje na da hannu a zanga-zangar da ake shirin yi a fadin kasar.

Da yake amincewa da ‘yancin da kundin tsarin mulkin Nijeriya, ya tanada ga ‘yan ƙasa na damar gudanar da taro ko zanga-zangar lumana, ya bukaci dukan ƙungiyoyin da ke shirya zanga-zangar da su yi wa kwamishinan ‘yansanda cikakken bayani a jiharsu, inda ake son gudanar da zanga-zangar.

Wannan ya ce zai rage hatsarin tashin hankali da lalata dukiya ko wasu ayyukan laifuka daga masu zanga-zangar tare da biyayya ga doka ba take haƙƙin wasu ba, inda ya ce shaida cewa suna sa ido tattare da barazanar zanga-zangar.

Leadership Hausa

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments