Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeIlimiLittafina yana ƙarfafawa Matasa Su Shiga Cikin ƙananan kasuwanci..Sulaiman Geidam

Littafina yana ƙarfafawa Matasa Su Shiga Cikin ƙananan kasuwanci..Sulaiman Geidam

Daga, Muhammad Sani Chinade, Damaturu

Wani marubutu  daga jihar Yobe, Suleiman Mohammed Jinjiri, ya wallafa wani littafi mai suna “Gina Rayuwa ta Hanyar Kananan Kasuwanci” wadda ya ce ya yi hakan ne domin tallafawa  matasa don su tsaya da kafafun su.

Marubucin ya bayyana hakan ne ga wakilinmu  a garin Damaturu dangane da kokarin da ya yi don ganin ya taimakawa ‘yan uwan sa matasa da zimmar in sun karata littafin zai jagorantar da su yadda za su gudanar da Sana’o’in da za su iya tsayawa da kafafun su don Kawar da zaman banza.

Shi dai Malam Sulaiman Mohammed Jinjiri matashi ne da ya yi karatu sa a jami’ar Maiduguri,  wadda ya ke karantar wa tare da gudanar da harkokin kasuwanci a garin Geidam da ke jihar Yobe.

Ya bayyana cewar, wannan Littafi na sa ya kunshi karfafa wa matasa gwiwa da su shiga kananan sana’o’i a matsayin hanyar inganta rayuwarsu da samun nasara a rayuwarsu.

Jinjiri ya ce ko da yake ya ji bukatar hakan kuma ya yarda cewa akwai littattafan kasuwanci da yawa na marubuta da dama, amma kadan ne kawai ke magana kan batun kasuwanci a Najeriya musamman jihar Yobe.

Ya bayyana cewa littafin ya zo da cikakken ilimin yadda ake fara kasuwanci, dabarun da ake bukata don gudanar da sana’o’i da kuma damammaki mai yawa da za su samu biyan bukata kan harkokin kasuwanci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments