Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiƊalibai Da Dama Sun Maƙale Cikin Baraguzan Ginin Makaranta A Jos

Ɗalibai Da Dama Sun Maƙale Cikin Baraguzan Ginin Makaranta A Jos

Wani ginin makaranta a yankin Busa Buji, ƙaramar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato, ya rufta, inda ya bar ɗalibai da dama a maƙale. Wannan mummunan al’amari ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na safe a yau Juma’a, yayin da ɗalibai ke tsaka da rubuta jarabawa.

Ginin makarantar Saint Academy ya yi ruftawar da ta jawo tsoro da firgici tsakanin iyayen ɗaliban, waɗanda suka yi ta tsere zuwa wurin da abin ya faru cikin ruɗani don ganin ko ya rutsa da ƴaƴansu.

A halin yanzu ana gudanar da aikin ceto tare da taimakon jami’an tsaro, ciki har da Sojojin da ƴan sanda. Motar ceto da aka kawo domin taimakawa cikin aikin ta maƙale a cikin ƙasa, wanda ya ƙara tsananta al’amuran. Akwai rahotannin da ba a tabbatar ba na mutuwar wasu daga cikin waɗanda suka makale, duk da cewa an kai wasu ɗalibai da suka ji raunin asibiti domin samun kulawa.

Sashen da ya rufta ya haɗa da azuzuwan ɗaliban SS1 SS2 da SS3 Hankalin jami’an ceto ya karkata wajen ceto waɗanda har yanzu suke maƙale da kuma ba da kulawar lafiya ga waɗanda suka ji rauni yayin wannan rahoto.

Aminiya

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments