Sunday, April 27, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiAn Tasa Keyar Tsohon Ministan Wutar Lantarki Zuwa Gidan Kaso

An Tasa Keyar Tsohon Ministan Wutar Lantarki Zuwa Gidan Kaso

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare tsohon ministan wutar lantarki, Saleh Mamman a gidan yari na Kuje da ke Abuja har sai an duba bukatar belinsa.

Kotu ta yanke hukuncin tura tsohon ministan wutar lantarki, Saleh Mamman, gidan yari, wanda ya yanke jiki ya fadi lokacin da ake zaman kotun.

A ranar Alhamis, 11 ga watan Yuli, mai shari’a James Omotosho, ya bayar da umarnin ne, biyo bayan gurfanar da Mamman a kotun kan tuhume-tuhume 12 da suka shafi halasta kudaden haram.

Alkalin kotun ya sanya ranar Juma’a 12 ga watan Yuli domin ci gaba da sauraren karar neman belinsa.

Bugu da kari, alkalin ya bayar da umarnin a tsare wanda ake kara a gidan yari na Kuje har sai an saurari karar.

Wanda ake tuhumar, wanda lauyansa ya bayyana cewa ba shi da lafiya, biyo bayan faduwa daga akwatin sauraren kara da ya yi.

Leadership Hausa

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments