Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiMun kashe kusan naira milyan 7 wajen inganta Harkar Lafiya==Hon Isah Umar

Mun kashe kusan naira milyan 7 wajen inganta Harkar Lafiya==Hon Isah Umar

Daga Rabiu Sanusi

Kimanin naira milyan bakwai ne harkar lafiya ta laqume a karamar hukumar Tudun Wada dake jihar Kano dan inganta harkokin Lafiyar Al’umma.

Kantoman riko na karamar hukumar Tudun Wada Hon Umar Isah Rugu-Rugu ne ya bayyana haka yayin bude wata karamar asibitin sha ka tafi daya gudana a garin Kwarin Goshi dake karamar hukumar Tudun Wadar.

Hon isah Umar yace matsayin su na shugabanin riko na jama’ar da Allah ya dora masu nauyin su, yazama dole su samar ma da Al’umma mafita ta hanyar inganta harkokin tsaro da lafiya.

Hon Rugu-Rugu ya kuma kara da cewa wannan kudiri na daya daga cikin yunkurin Gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na kawo Sauyi ga al’ummar Jihar ta fanni daban-daban.

“Kowa yasani a wannan karamar hukumar tamu ta Tudun Wada a lokacin baya bamu mun samu shugabanin da basu da kishin Al’umma, yazuwan mu yanzu yazama dolen mu samar da sauyi ta ko ina dan jama’ar mu su samu rayuwa mai kyau.

Kantoman yace basu ce zasu cika asibitoci da kayan aiki ba, amma kuma zsauyi bakin kokarin su na sauya fasalin guraren da babu kulawa.

Mafi yawan asibitocin da Kantoman ya gyara a garuruwan da suka samu kulawar ance ba wannan Gwamnatin ta samar dasuba, sai da bayan gida asibitocin kimanin shekaru takwas a baya na tsohuwa gwamnatin baya ba’a bude su ba.

” wannan ya bamu damar ganin cewa koda bamu muka gina ba anyi sune dan Al’umma kuma Al’ummar mu dan haka muka yanke shawarar gyara su tare da zuba masu kayan aiki da taimakon jama’ar mu ta fannin lafiya.

Bayan haka kuma kantoman ya bukaci sauran jami’an tsaro dasu taimaka wajen basu hadin kai na kula da cigaba da kawo zaman Lafiya a wannan yanki nasu.

Wasu daga cikin garuruwan da zasu amfana da wannan kayan lafiya da gyaran na sha katafi sun hadar da Kauyukan Kwarin Goshi, Sunusi,Kyangyaran Tuku da dai sauran su.

Haka zalika kantoman yace wannan kayan da suka saya dan taimakawa Al’ummar sa bawai jihar Kano ta basuba sun kokarta ne wajen abinda suke samu daga harajin karamar hukumar su da kuma tallafin kwabo da sisi daga masu kishin tafiyar su.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments