Daga Rabiu Sanusi
An yi kira ga Matasa a jihar Kano, musamman wanda suka kamalla makaranta da ba su samu aiki ba, da su rungumi sana’o’i don kaucewa zaman-kashe-wando,
Wannan kiran na zuwa ne daga bakin babban daraktan hukumar samar da Magunguna da Kayan Asibiti ta Jihar Kano, Famasist Gali Sule ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a gurin bikin cika shekara 10 da kammala makaranta da Kungiyar Tsofaffin Daliban Makarantun Sakandiren Kimiyya da fassha ta Jihar Kano (KASSOSA) reshen Makarantar Kimiyya da ke garin Dawakin Kudu Aji Na shekarar 2014 (Class 2014) suka shirya a ranar lahadin nan.
Darakta-Janar din ya ce saboda matsin tattalin arziki da ake fama da shi a Qasar nan, da kuma durqushewar masana’antu da kamfanoni, wanda hakan ya jawo karuwar rashin aikin yi.
“zai fi kyau m tallafawa matasan mu dan su kama sana’a da zata kara rufawa kansu asiri.”
Famasist Gali Sule ya qara da cewa gwamnatin jihar Kano, qarqashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, na iya bakin kokarin ta dan samar wa da jama’a abun yi, ta hanyar ba da jari ga dumbin matasa Maza da Mata tare da gina guraren koyar da sana’o’i guda 10, hadi da gyarawa da kuma bude wadanda suka lalace.
Daga nan sai ya kuma yabawa Kungiyar KASSOSA qarqashi Shugabanta na Qasa, Alh. Balarabe Nuhu Jallah, bisa koyar da sana’o’i ga ‘yan Qungiyar da ba su sami aiki ba, da kuma ba su tallafi dan dogaro da kai
Haka kuma Daraktan-Janar na DMCSA din ya yi kira ga sauran rassan kungiyar tsofaffin Xaliban da su yi koyi da Uwar Qungiyar ta Qasa wajen koyawa mambobin su sana’o’i da ba su tallafin jari.
Shugaban kungiyar ta KASSOSA Aji Na 2014, Mal.Abubakar Idris Yarima ya godewa bakin da suka sami damar halartar taron duk da irin hidindumu da ke gabansu.