Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiKasar Nijeriya, Saudiyya Sun Kulla Yarjejeniyar Yakar Yunwa

Kasar Nijeriya, Saudiyya Sun Kulla Yarjejeniyar Yakar Yunwa

Gwamnatin Tarayya ta sanar da kulla wata yarjejeniyar samar da abinci da kasar Saudi Arabiya, a kokarin da ake yi na fatattakar yunwa a fadin duniya.

Ministan noma da abinci, Abubakar Kyari ne, ya bayyana hakan ta shafinsa na X, yana mai cewa yarjejeniyar za ta bai wa Saudi Arabiya damar kafa kamfanin samar da kayayyakin aikin gona a Nijeriya.

Ya ce an cimma wannan matsaya ne a yayin taron ganawa da hukumomin kasashen biyu suka gudanar.

Baya ga haka kuma, Kyari ya ce kasashen biyu sun amince da kulla cinikayyar jan nama da kuma waken suya.

Nijeriya ce dai za ta sayarwa da Saudiyya tan dubu 200 na jan nama kowacce shekara, yayin da za ta sayar mata da tan miliyan daya na waken suya a duk shekara.

Nineriya na cikin jerin kasashen da majalisar dinkin duniya, ta ayyana cikin masu fama da yunwa da kuma karancin abinci.

Leadership Hausa

 

 

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments