Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeTsaroHarin Ƙunar Ɓakin Wake a Borno Ya Halaka Mutum 6

Harin Ƙunar Ɓakin Wake a Borno Ya Halaka Mutum 6

Wasu ‘yan ƙunar bakin wake biyu sun tayar da bama-bamai a wurin shagalin bikin aure da ke Tashar Mararaba, kusa da hukumar kashe gobara a garin Gwoza da ke jihar Borno, inda suka kashe mutane shida da suka halarci taron auren tare da jikkata wasu da dama.

A cewar wani wanda ya tsira da ransa, ‘yar ƙunar baƙin waken ta farko tana ɗauke da jariri kuma matashiya ce, mai kimanin shekaru 20, inda ta zo kamar baƙuwa a taron auren kana ta tayar da bam din.

Yayin da ake kokarin birne mutanen da suka mutu, wani dan ƙunar baƙin waken da ya yi kama da mai jimami ya tayar da bam na biyu a wurin jana’izar, inda ya kashe mutum guda.

Waɗanda suka samu raunuka tuni an garzaya da su babban asibitin Gwoza, don ba su kulawa, inda sojoji kuma suka saka dokar hana fita a Gwoza, sakamakon mummunan lamarin.

Leadership Hausa

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments