By Aliyu Bala Gerengi, Gombe
Shugaban Karamar Hukumar Dukku ta Jihar Gombe, Honarabul Abubakar Adamu, ya shirya taron tattaunawa da shugabannin gargajiya, manoma, makiyaya, jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki, domin lalubo hanyoyin magance matsalolin tsaro da ke kunno kai a yankin.
An gudanar da taron ne a fadar Hakimin Bozonsulwa da ke Waziri ta Kudu, inda aka mai da hankali kan samar da mafita mai dorewa ga matsalolin da ka iya kawo barazana ga zaman lafiya da tsaro, musamman rashin fahimtar juna tsakanin manoma da makiyaya.
Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Karamar Hukumar Dukku, Honarabul Abubakar Adamu, ya ce ya gayyaci jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin tattauna matsalolin da ake fuskanta tare da samar da hanyoyin da za su taimaka wajen dakile rikice-rikice da tabbatar da zaman lafiya a yankin.
A nasa jawabin maraba, Hakimin Bozonsulwa, Alhaji Kamalu Hayatu Gurama, ya yaba wa Shugaban Karamar Hukumar Dukku da jami’an tsaro bisa shirya taron wayar da kan manoma da makiyaya kan muhimmancin zaman lafiya da fahimtar juna.
Ya ce irin wannan tattaunawa na da muhimmanci wajen rage rashin fahimtar juna da kuma hana ayyukan da ka iya haifar da tashin hankali tsakanin al’ummomin yankin.
Shi ma Shugaban Miyetti Allah Kautal Hore na Jihar Gombe, Dakta Ardo Chindo Abubakar, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki, manoma, makiyaya da jami’an tsaro da su kara kaimi wajen wayar da kan matasa game da muhimmancin zaman lafiya da zaman tare.
Dakta Chindo Abubakar ya tabbatar da cewa kwamitinsa zai ci gaba da hada kai da hukumomin da abin ya shafa wajen tantancewa da kafa iyakokin hanyoyin da shanu ke bi, tare da tabbatar da bin hanyoyin kiwo da aka amince da su, domin dakile rikice-rikice a fadin jihar.
A jawabansu daban-daban, Jami’in ’Yan Sandan da ke kula da Sashen ’Yan Sanda na Dukku, ASP Nura Sulaiman, da wakilan sauran hukumomin tsaro, sun bukaci manoma da makiyaya da su rungumi tattaunawa a matsayin hanya mafi dacewa wajen warware sabanin da ke tsakaninsu, maimakon daukar mataki da zai iya haifar da rikici.
Jami’an tsaron sun kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki a yankin da su wayar da kan al’ummominsu kan muhimmancin kiyaye zaman lafiya da tsaro.
A jawabinsa na karshe, Shugaban Karamar Hukumar Dukku, Honarabul Abubakar Adamu, ya gode wa Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, bisa kokarinsa na samar da ci gaba, musamman ayyukan da ake gudanarwa a Wawa-Zange Grazing Reserve.
Ya kuma yi kira ga matasan Fulani da su guji daukar doka a hannunsu, tare da yin gargadi kan kutsawa cikin gonakin manoma ta hanyar kai dabbobi cikin gonaki.
Shugaban ya kuma bukaci Kwamitin aiwatar da yarjejeniyar tsakanin manoma da makiyaya da ya ci gaba da tantancewa da sanya alamar iyakokin hanyoyin shanu da wuraren kiwo a cikin Karamar Hukumar Dukku, domin hana rikice-rikice da tabbatar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin manoma da makiyaya.


