By Aliyu Bala Gerengi, Gombe
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai bar Abuja a yau zuwa Turai domin fara hutun shekara-shekara na tsawon makonni uku.
A cewar wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, London a Birtaniya ce za ta kasance zangon farko na ziyarar shugaban ƙasar.
Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu zai shafe makonni uku yana hutun shekara, kafin ya dawo Najeriya.
Ana sa ran shugaban ƙasar zai dawo gida domin ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati, tare da shiga shirye-shiryen yaƙin neman zaɓen zaɓen watan Janairun 2027.
Sanarwar ta bayyana cewa tafiyar na daga cikin hutun shekara-shekara na Shugaba Tinubu.


