Thursday, May 15, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiZulum Ya Haramta Sayar Da Barasa A Borno, A Yunkurin Yaki Da...

Zulum Ya Haramta Sayar Da Barasa A Borno, A Yunkurin Yaki Da Masu Aikata Muggan Laifuka

Daga Sani Gazas Chinade Damaturu

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya haramta sayar da barasa da kuma shan barasa a hukumance a fadin jihar, a wani sabon lamari na kariya da cin zarafin ga al’umma da shan barasar ke haifarwa.

Gwamnan ya  bayyana hakan ne a Maiduguri a yayin kaddamar da wani kwamiti wanda aka dorawa aikin yaki da shan haramtattun kwayoyin sa maye da kuma haramtattun  otal-otal, irin na karuwai da maboyar masu aikata muggan laifuffuka a babban birnin jihar da kewaye.

Gwamna Zulum ya bayyana cewa haramcin ya biyo bayan matsalolin tsaro da ke da nasaba da shaye-shaye da suka hada da fadace-fadace, karuwanci, shaye-shaye, fashi da makami, da kuma ’yan daba, wadanda a cewarsa suna janyo tarbarewar tsaro salwantar da dukiyoyi da makamantan haka.

Gwamnan ya ce an baiwa cikakken ikon ga hadakar jami’an soji, jami’an ‘yan sanda, jami’an tsaron farar hula, da jami’an Civilian Joint Task Force (JTF) wajen hada gwiwa domin kawar da ayyukan ta’addanci da na badala a tsakanin al’umma da ke haifar da barazanar tsaro.

Zulum ya kuma zargi wasu jami’an tsaron kasar da suke aiki da kuma wadanda aka sallame su da zargin aikata munanan dabi’u a tsakanin farar hula, lamarin da ya ce yana samar da tsattsauran ra’ayi, karuwanci, da kan haifar da rashin tsaro.

“Na ji dadin ganin wakilan sojoji, ‘yan sanda, da sauran bangarorin jami’an tsaro a wannan wuri. Bari in fayyace cewa yawancin waÉ—annan munanan ayyukan ana aikata su ne ta hanyar korarrun jami’an tsaro kai har ma da wasu daga cikin jami’an tsaron da ke aiki a yanzu, tare da wasu fararen hula,” in ji Zulum.

“Idan har ana son kawar da ta’addanci, da sauran wuraren aikata ta’assa a birnin  Maiduguri da jihar, dole ne a hukunta kowa.”

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments