Daga Abdullahi Inuwa
A cikin wani sabon salo na siyasa gabannin zaɓen shekarar 2027, tsohon Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Mohammed Adamu, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Da yake jawabi a wani taron gagarumi da aka gudanar a Lafia ranar Litinin, Adamu ya sha alwashin kawo “doka, tsaro da ingantaccen shugabanci” ga jihar, yana mai cewa zai yi amfani da kwarewarsa ta shekaru da dama a fannin tsaro da jagoranci.
“Na yi wa Najeriya hidima a matakin koli na aikin tsaro. Yanzu lokaci ya yi da zan dawo in yi wa al’ummata hidima, domin tabbatar da zaman lafiya, cigaba da wadata ga kowane ɗan Nasarawa,” inji shi yayin da magoya bayansa suka rika shewa da murna.
Wasu jiga-jigan jam’iyyar sun bayyana cewa fitowar Adamu takara ya sauya taswirar siyasar jihar, duba da irin ƙwarewa da haɗin kan da yake da shi a tsakanin al’ummomin Nasarawa.
Masu sharhi na ganin cewa ana sa ran fafatawar APC za ta yi zafi sosai, ganin cewa akwai manyan masu ruwa da tsaki da suka riga suka nuna sha’awarsu kafin Adamu ya bayyana.
Yanzu haka idanu sun karkata zuwa Nasarawa, domin ganin ko tsohon babban jami’in ‘yan sanda zai iya tara goyon bayan da zai kai shi ga samun tikitin jam’iyyar APC tare da kafa tarihi.