Wani bidiyo mai tayar da hankali da ke nuna wani matashi yana lafaza azzakarin akuya domin yin suna a kafar TikTok ya jawo hankalin Jami’an Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, inda suka kama shi.
Wanda ake zargi, Shamsu Yakubu mai shekara 24 daga karamar hukumar Dawakin Kudu, an kama shi ne a ranar Talata bayan bidiyon ya karaɗe shafukan sada zumunta, yana nuna yadda ya umarci wani ya dauke shi bidiyo a lokacin da yake aikata wannan mummunan aiki.
Domin neman shahara a yanar gizo, an ga Yakubu yana sanya bakinsa a gabannin akuya, abin da ya fusata mazauna yankin da suka kusan dukan sa, kafin wani jagoran al’umma ya kai karar sa ga hukumar Hisbah.
A lokacin da ake yi masa tambayoyi, Yakubu ya musanta cewa ya lafaza azzakarin dabbobi. Ya ce: “Na saka bakina ne kusa da wajen, amma ban taɓa aikata irin haka ba a rayuwata. Na yi ne kawai don in yi fice.”
Sai dai Hukumar Hisbah ba ta dauki maganar da wasa ba. Mataimakin Kwamanda-Janar, Sheikh Aminuddeen Abubakar, ya bayyana wannan aiki a matsayin “marar kunya kuma sabawa addini”, inda ya ce za a kai Yakubu gwajin kwakwalwa da kuma kwayoyi.
“Shekaran akuya za a kai ta asibitin dabbobi don a tabbatar da ko ta kamu da wata cuta daga hannun wanda ake zargi,” in ji Sheikh Aminuddeen.
Ya kuma gargadi matasa masu bin irin wannan hanyar neman suna: “Duk wanda aka kama yana aikata abubuwa marasa tarbiyya domin yin fice a TikTok, to za a cafke shi kuma a hukunta shi yadda ya kamata.”
Wannan lamari ya biyo bayan wani saurayi daga Kano da ake kira “Kabiru 2-Pac” wanda shima ya shahara kwanan nan a kafar TikTok bayan ya yi wanka da ruwan bola yana daukar bidiyo, abin da ke kara yawaitar dabi’un ban tsoro a tsakanin matasa.
Daily News 24