Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiGwamnatin Yobe Ta Kaddamar da Sabon Rumbun Wuta 60MVA A Damaturu

Gwamnatin Yobe Ta Kaddamar da Sabon Rumbun Wuta 60MVA A Damaturu

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

Sakataren Gwamnatin Jihar Yobe, Baba Malam Wali ya ziyarci sabon 60MVA 132/33KV Mobile Injection Transformer da aka kawo tare da haɗin gwiwar Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN), a tashar 330/132/33KV sub-station da ke Damaturu, a ranar Laraba 16 ga Afrilu, 2024.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Sakataren Gwamnatin Jihar Yobe, Shuaibu Abdullahi, ya fitar, Alhaji Baba Malam Wali ya ce wannan muhimmin ci gaba na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar domin inganta samar da wutar lantarki, tare da bin hangen nesan Gwamna Hon. Mai Mala Buni na gina manyan ababen more rayuwa da kuma farfaɗo da tattalin arzikin jihar.

Ana sa ran wannan sabon transformer zai ƙara ƙarfin samar da wutar lantarki a jihar Yobe matuƙa, wanda hakan zai magance matsalolin da ake fuskanta tun da dadewa, da ƙarfafa yanayi mai kyau ga harkokin zamantakewa da tattalin arziki.

A cewarsa, ta hanyar saka hannun jari a irin wannan muhimmin aikin, gwamnati na da nufin haɓaka ci gaban tattalin arziki, jawo masu zuba jari, da kuma inganta rayuwar al’umma. Wannan aikin yana tabbatar da yadda gwamnati ke da kishin cika alkawuranta da kawo cigaba mai dorewa.

A ƙarƙashin jagorancin Gwamna Buni, gwamnatin jihar Yobe na aiki tukuru wajen cika bukatun jama’a, kuma wannan ci gaba na baya-bayan nan shaida ne a fili na irin ƙoƙarin da ake yi.

Aiwatar da wannan aiki cikin nasara zai kawo gagarumar fa’ida da suka haɗa da ƙarin damar tattalin arziki, kyautata harkokin kasuwanci, da kuma sauƙaƙa samun manyan ayyuka ga al’ummar jihar gaba ɗaya.

Saboda haka, wannan ci gaba wani babban mataki ne a cikin tafiyar cimma burin ci gaban jihar da kuma hangen ganin Yobe mai albarka.

Sakataren Gwamnatin Jihar ya samu rakiyar Kwamishinan Ma’aikatar Ayyuka, Injiniya Umaru Wakili Duddaye, da Babban Manajan Hukumar Wutar Lantarki ta Karkara ta Jihar Yobe, Injiniya Umara Mustapha Goneri.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments