Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiTashin Bam a Borno Ya Kashe Mutum 8, Ya Jikkata 21, Zulum...

Tashin Bam a Borno Ya Kashe Mutum 8, Ya Jikkata 21, Zulum Ya Kai Ta’aziyya

“Mun gamsu da martanin manyan hafsoshin tsaro” – Zulum

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya kai ta’aziyya da jaje ga mutane 21 da suka jikkata sakamakon fashewar bam da ake zargin ‘yan Boko Haram ne suka dasa a hanyar Maiduguri zuwa Damboa a ranar Asabar.

Cikin wadanda lamarin ya rutsa da su, 14 sun samu mummunan rauni, yayin da 7 suka samu raunuka kadan, kuma ana kula da su a Asibitin Kwararru na Maiduguri.

Yayin da yake jaje, Gwamna Zulum ya nuna alhini tare da nuna goyon baya ga iyalan mutane 8 da suka rasa rayukansu a harin.

“Abin takaici ne ganin irin wannan abu yana faruwa a wannan lokaci. Tun shekara daya da ta gabata ko fiye, ba mu fuskanci harin bam da aka dasa ba (IED). Hanyar ta kasance a rufe har tsawon kusan wata daya, kuma na yi imani wannan ne ya bai wa ‘yan ta’addan damar dasa bama-baman,” in ji Zulum.

Gwamnan ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da tallafawa jami’an tsaro tare da bukatar karin tsaro a hanyar don hana irin haka faruwa a gaba.

“Ina kira ga sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro da su kara tsaurara tsaro a wannan hanya don hana maimaituwar irin wannan lamari,” Zulum ya nanata.

“Gwamnatin Jihar Borno za ta ci gaba da hadin gwiwa da rundunar sojojin Najeriya da gwamnatin tarayya wajen dakile matsalar ta’addanci. Ina tabbatar wa al’ummar Jihar Borno cewa, Insha Allah, a karkashin shugabancina, ba za mu bari matsalar tsaro ta kara ta’azzara ba.”

“Za mu kara bai wa jami’an tsaro goyon baya, kuma za mu kara karfafa gwiwar matasa masu aikin sa-kai da ke fafutuka tare da sojoji.”

…Mun gamsu da martanin hafsoshin tsaro – Zulum

A wani bangare, Gwamna Babagana Umara Zulum ya bayyana gamsuwa da sakamakon ganawar da aka yi da hafsoshin tsaro a ranar Alhamis a birnin Abuja.

Da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a Maiduguri ranar Asabar bayan ziyarar jaje ga wadanda suka jikkata, Zulum ya ce, “Tattaunawarmu a kwamitin tsaro ba ta da matsala; mun bayyana damuwarmu cewa ayyukan Boko Haram na kara karfi a Jihar Borno, don haka gwamnatin jiha, rundunar sojoji da sauran masu ruwa da tsaki su hada kai don dakile wannan barazana.”

Ya kara da cewa, “Abin da yafi muhimmanci, mun je Abuja, mun gana da hafsoshin tsaro kuma sun ba mu tabbacin za su yi duk mai yiwuwa wajen shawo kan lamarin. Muna matukar gamsuwa da martaninsu.”

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments