Daga Abdullahi Inuwa
Sabon Tsari Zai Inganta Tsaro, Ciniki da Kara Kudaden Shiga
Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta bayyana sabon shiri na sauya fasalin dukkan tashoshin iyakoki a fadin kasar ta hanyar amfani da fasahar geospatial domin kara tsaro da saukaka harkokin ciniki.
Wannan muhimmin ci gaba an bayyana shi ne a taron manema labarai da aka gudanar a ofishin Kwastam da ke Katsina a ranar 8 ga Afrilu, 2025. Wannan taron ya biyo bayan ziyarar aiki da Kwamptrola Janar mai kula da Yankin B (Zone B), A.A.S. Oloyede ya kai.
ACG Oloyede ya bayyana cewa wannan mataki wani babban cigaba ne wajen daidaita ayyukan kula da iyakoki na Najeriya da tsarin duniya. Ya ce sabon tsarin zai rage jinkiri, ya kara karbar kudaden shiga, kuma ya dakile cin hanci da rashawa da kara gaskiya da bayyana gaskiya a ayyukan hukumar. “Muna shiga sabon zamani na tsaron kasa da saukaka harkokin kasuwanci cikin basira,” in ji shi.
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda (Ph.D.), ya yaba da wannan ci gaban, yana mai cewa lokaci ya yi da ake bukatar irin wannan tsari. Yayin karbar bakuncin ACG a gidan gwamnati, Gwamna Radda ya bayyana irin rawar da wannan fasaha za ta taka wajen bunkasa tattalin arziki, tsaron kasa, da ci gaban al’ummomin iyaka. “Wannan kirkira za ta inganta tattara bayanan leken asiri da tabbatar da tsaron iyakokinmu cikin sauki,” in ji shi.
ACG Oloyede ya kuma yabawa Kwamanda Abba-Aji Idriss, wanda ke jagorantar ofishin Katsina, bisa shugabanci nagari da hadin kai tsakanin jami’an kwastam da sauran hukumomi, masu ruwa da tsaki da jami’an gwamnati a yankin.
Wannan shiri na sauya fasali wani bangare ne na tsare-tsaren hukumar Kwastam na daukar fasahar zamani domin inganta ayyuka da kara gaskiya, tare da cika bukatun tattalin arzikin duniya na yau.