Daga Abdullahi Inuwa
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya samu karin girmamawa ta kasa da kasa bayan an nada shi a matsayin Jakadan SDGs na Duniya (UN Sustainable Development Goals Global Champion) saboda gudummawar da ya bayar wajen wanzar da zaman lafiya, tallafin jinƙai da ci gaban ɗorewa a arewa maso gabashin Najeriya.
An gabatar da lambar yabon ne a wani taron shekara-shekara na NGO Founders Global Network da aka gudanar a Munich, ƙasar Jamus, ranar Juma’a.
NGO Founders Global Network ita ce babbar ƙungiyar haɗin gwiwar ƙetaren ƙasa da ke ƙarfafa ayyukan ƙungiyoyi masu zaman kansu da ƙungiyoyin agaji domin cika burin SDGs na Majalisar Dinkin Duniya don amfanin ɗan’adam da al’umma baki ɗaya.
An karrama Gwamna Zulum ne bisa ƙoƙarinsa na gina garuruwan da rikicin Boko Haram ya lalata, da inganta fannin ilimi, lafiya, ababen more rayuwa, da hanyoyin samun abin dogaro, da kuma daidaita dokokin jihar da tsare-tsaren ci gaban duniya na 2030.
Zulum ya taɓa samun lambobin yabo da dama, ciki har da Forbes African Leadership Award, Gwamnan Shekara na Afirka (a fannin Ilimi da Ci gaban Jama’a) na 2023 daga African Leadership Magazine, da kuma lambar yabo ta biyu mafi girma a Nijar wato “De Grand Officer Dans l’Ordre”.
A madadinsa, Mataimakin Gwamnan Borno, Umar Usman Kadafur, ne ya karɓi lambar yabon, inda ya nuna godiya ga masu shirya taron bisa wannan karramawa, tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da bada shugabanci mai inganci domin inganta rayuwar al’ummar Borno.
Mista Kadafur ya samu rakiyar Dr Mairo Mandara, Babbar Mashawarciyar Gwamna kuma Mai Tsara Hulɗa kan Ci Gaban Dorewa da Ayyukan Jinƙai.