Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiSAƘON GAISUWAR SALLAH EID-EL-FITR GA AL'UMMAR MUSULMIN NIJERIYA

SAƘON GAISUWAR SALLAH EID-EL-FITR GA AL’UMMAR MUSULMIN NIJERIYA

Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) na isar da saƙonta na taya murna ga ɗaukacin al’ummar Musulmin Nijeriya da na duniya bakiɗaya, albarkacin kammala azumin watan Ramadan na 2025 da kuma murnar gudanar da sallar Eid-el-Fitr da aka yi. Allah Ya sa wannan lokaci ya zama mai albarka, lokacin farinciki da nazari kan ayyukan da muka yi da wanda ba mu yi ba, tare da addu’o’i domin samun ɗorewar zaman lafiya, da samun dacewa da rahamar Ubangiji ga iyalanmu da ɗaukacin Musulmi. Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya karɓi ibadarmu ta azumi da muka gabatar, Ya kuma yafe mana kurakuran da muka yi a cikinsa. Allah Ya sa dukkan ayyukanmu na ibada da addu’o’inmu cikin Ramadan sun zama karɓaɓɓu. Da fatan Allah zai cigaba da buɗa mana hanyoyin Sa na rahama da yalwa a cikin sauran kwanaki da watannin da suka rage mana. Amin.

Sannan, muna tunatar da ýan’uwa Musulmi da mu cigaba da ayyukan ibada kamar yadda muka kasance muna yi a cikin Ramadan, domin cigaba da samun lada daga Allah Maɗaukakin Sarki. A cikin watan Ramadan Musulmi sun gudanar da azumi ta hanyar ƙauracewa abinci da abin sha da duk wata sha’awa ta rayuwa, daga ketowar alfijir zuwa faɗuwar rana, yayin da suka mayar da hankali kan ayyukan ibada da neman ƙarin kusanci ga Ubangiji. Don haka, bai kamata waɗannan ayyuka na alheri su taƙaita a Ramadan ba. A yayin da muke gudanar da shagulgulan ƙaramar Sallah, JNI, na tunatar da ɗaukacin al’ummar Musulmi kada su manta da azumin Sitta-Shawwal da ake yi cikin wannan wata, wato azumin ranakun shida da ake yi bayan Ramadan, kamar yadda Ma’aikin Allah Annabi Muhammad (SAW) ya kwaɗaitar da mu. Kada mu manta Ubangijin Ramadan, rayayye ne har cikin sauran watannin, don haka mu cigaba da kiyaye dokokinSa a kodayaushe. Sannan, muna ƙara tunatar da junanmu muhimmancin da ke cikin riƙo da Alƙur’ani Mai Girma, a matsayin martaba da darajar al’ummar Musulmi. Abu mai muhimmanci harwayau, mu cigaba da neman ilimi. Babu shakka, watan Ramadan ya kasance muhimmin lokaci na neman ilimi game da koyarwar addinin Musulunci, da fatan za mu ɗore da nuna ƙishir ruwan neman ilimi har zuwa bayan Ramadan.

A ƙarshe, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, kuma Babban Shugaban JNI ya yaba da ƙoƙarin da Gwamnatin Jihar Kano da jami’an tsaro suka nuna wajen hana kai wa juna hare-hare a cikin Jihar Kano. Ya kuma yaba wa masarautar Kano game da dakatar da hawan Daba da ta yi, domin kaucewa samun hatsaniya. A yayin da muke sa’ido da bibiyar abubuwan da ke faruwa a Jihar Edo, muna masu yabawa da ƙoƙarin da Gwamnatin Jihar Edo ta yi game da kisan gillar da aka yi wa wasu Musulmi ýan Arewa su 16 a Uromi, tare da yin kira ga Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Edo da lallai a biya diyya ga iyalan waɗanda aka kashe a Uromi, don tabbatar da adalci da kiyaye haƙƙokin juna.

JNI na taya al’ummar Musulmi fatan an yi azumin Ramadan karɓaɓɓe, da kuma fatan an yi Sallah lafiya.

Prof. Khalid Abubakar Aliyu
Babban Sakataren, JNI

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments